in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko Jamus za ta canja manufarta kan Sin bayan babban zaben da aka yi?
2017-09-25 10:41:31 cri

A jiya Lahadi 24 ga watan Satumban da muke ciki, agogon kasar Jamus ne, aka gudanar da babban zaben majalisar dokokin kasar, bayan zaben, an kidiya kuri'un da aka kada a mataki na farko, daga baya an sanar da sakamakon da ke tabbatar da cewa, Angela Merkel, wadda ta ke rika mulkin kasar ta Jamus har tsawon shekaru 12 za ta lashe zaben, wato za ta ci gaba da kasancewa shugabar gwamnatin kasar ,kana ana zaton Merkel ba za ta yi wannan canji game da manufar gwamnatinta kan kasar Sin ba.

Yayin da ya zanta da manema labarai a kwanakin baya, mataimakin ministan kula da tattalin arziki da makamashi da sufuri da raya kasa na lardin Hesse-Darmstadt dake tsakiyar kasar Jamus Norbert Noisser ya bayyana cewa, dalilin da ya sa ya ke ganin cewa, gwamnatin kasarsa ba za ta canja manufarta kan kasar Sin bayan babban zaben ba shi ne domin kasar Sin ta riga ta kasance muhimmiyar abokiyar ciniki ta Jamus a Asiya, har ma tana gudanar da huldar hadin gwiwa dake tsakaninta da Jamus a fannonin tattalin arziki da zuba jari da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da cudanyar al'adu da sauransu. Noisser yana mai cewa, "Ko shakka babu gwamnatin kasar Jamus, tsohuwa ko sabuwa, za ta sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin a wadannan fannoni, kuma za ta kara mai da hankali kan wannan batu, ba zai yiyu ba gwamnatin Jamus ta kau da kai ga zumunci da huldar abokantaka dake tsakaninta da kasar Sin ba."

A halin da ake ciki yanzu, ana gudanar da tsarin hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu wato Sin da Jamus bisa matakai sama da 71, misali shawarwari tsakanin gwamnatoci, da shawarwarin diplomasiyya da tsaro, shawarwari kan harkokin kudi da al'adu da sauransu dake tsakanin sassan biyu, kana ana kokarin habaka hadin gwiwa dake tsakaninsu a fannonin kimiyya da fasaha da sarrafa albarkatun man fetur da kuma yanar gizo.

Shugaban kungiyar sada zumunta dake tsakanin Jamus da Sin ta Dusseldorf ta Jamsu Dieter Boning yana ganin cewa, ko shakka babu huldar abokantaka da aka kulla tsakanin Sin da Jamus bisa manyan tsare-tsare za ta taka muhimmiyar rawa a harkokin diplomasiyyar da sabuwar gwamnatin kasar ta Jamus za ta yi, a saboda haka babban zaben da aka yi ba zai yi wani tasiri ga manufar Jamus kan kasar Sin ba, inda ya bayyana cewa, "Hakika ba zai yiyu ba sabuwar gwamnatin Jamus ta canja manufarta kan kasar Sin, saboda kusan daukacin jam'iyyun kasar ta Jamus sun cimma matsaya guda cewa, ba ma kawai kasar Sin abokiyar tattalin arziki ta Jamus ba ce, kana abokiyar siyasar Jamus ce, musamman ma tun bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya hau karagar mulki a Amurka, haka kuma su ma al'ummun kasar Jamus su ma sun lura da wannan lamari."

Masani kan kasar Sin na Jamus Wolfram Adolphi ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasashen Sin da Jamus suna gudanar da cudanya dake tsakaninsu yadda ya kamata, musamman ma a fannin tattalin arziki, yana mai cewa, "Na hakikan ce cewa, kasashen biyu wato Sin da Jamsu za su ci gaba da gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu yadda ya kamata bayan babban zaben da aka yi jiya, misali a fannonin tattalin arziki da ciniki da kuma siyasa, a sa'i daya kuma, ina fatan Jamus za ta kara tattaunawa da kasar Sin kan yadda za a cimma burin samun dauwamammen ci gaba a fadin duniya baki daya."

Mai madaba'ar littafi na kamfanin madabba'ar litattafan Jamus da Sin na Jamus Michael Ruhland shi ma yana cike da imani kan makomar huldar dake tsakanin Jamus da Sin, inda ya bayyana cewa, "Kafin shekaru sama da dari daya, idan ana son zuwa kasar Sin daga kasar Jamus cikin jirgin ruwa, sai an kwashe kusan makonni shida ko takwas, ko ma watanni uku, amma yanzu muna ana iya zuwa birnin Beijing daga Dusseldorf ta jirgin sama cikin sa'o'i goma kawai, yanzu ana iya tafiya daga wani wuri zuwa wani cikin sauki, har ma a gudanar da cudanya dake tsakanin al'ummomin kasashen duniya, a don haka ina cike da imani kan ci gaban hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Jamus."

Michael Ruhland ya kara da cewa, yanzu haka nan fuskantar rashin tabbas a kasashen duniya, kamata ya yi Sin da Jamus su kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu domin bude wani sabon babi a wannan fannin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China