A wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Pentagon din ta sanar tace, wannan ne karon farko a karni na ashirin da daya, da jiragen yakin Amurkar suka yi nisan zango kusa da Koriya ta Arewar, matakin tura jiragen ya faru ne domin nuna cewa Amurkar da gaske take wajen maganin halayyar kunnen kashi da Koriya ta Arewa ke nunawa game da batun gwajin makamanta na Nukiliya.
Dama dai a cikin jawabin da ya gabatar a taron MDD, shugaban Amurkar Donald Trump a ranar Talata yayi barazanar cewa, Amurkar bata da wani zabi illa ta lalata shirin makaman na nukilyar Koriya ta arewa domin kare kanta da kawayenta.
A ranar Juma'ar data gabata, kasar Sin ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki dasu guji daukar duk wani mataki da zai iya dagular al'amurra game da batun zirin Koriya.