Nkurunziza, ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi takardar aiki daga sabon jakadan kasar Sin dake Brundi mista Li Changlin a fadar shugaban kasar, inda ya kara da cewa, kasarsa na fatan kara neman sabbin hanyoyi na hada kai tare da Sin, kana kasarsa na maraba da kamfanonin kasar Sin da su zo kasar Brundi don zuba jari, ya bayyana fatansa na kara ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba.
A nasa bangare, jakada Li ya nuna yabo kan nasarar da kasar Brundi ta samu wajen inganta zaman lafiya da tsaro, da inganta samun jituwar al'umma da raya tattalin arzikin kasa da dai sauransu, ya kuma bayyana cewa, yana son yin kokari tare da bangaren Brundi a cikin wa'adin aikinsa, don zurfafa dangantakar hadin kai ta samun moriyar juna a tsakanin Sin da Brundi.(Bilkisu)