in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsibirin Pingtan na Fujian ya samu babban ci gaba bayan ziyarar Xi
2017-09-22 10:09:08 cri

A farkon watan Nuwambar shekarar 2014, babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a tsibirin Pingtan na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin, inda ya jaddada cewa, tsibirin muhimmin wuri ne da ake gudanar da hadin gwiwa a tsakanin lardunan Fujian da Taiwan, shi ma muhimmin wuri ne da ake aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen ketare na kasar Sin, a saboda haka kamata ya yi a kara sanya kokari matuka domin ciyar da tattalin arzikin tsibirin gaba, musamman ma wajen yawon bude ido.

Tsibirin Pingtan yana sauka ne a zirin Taiwan dake tsakanin babban yankin kasar Sin da tsibirin Taiwan na kasar, a sakamakon haka, ya kan gamu da guguwar iska a duk tsawon shekara, tsohon shugaban hukumar dazuka ta yankin gwajin tattalin arzikin Pingtan Lin Qingxing ya gaya mana cewa, "Babban sakarare Xi Jinping ya taba yin aiki a lardin Fujian cikin dogon lokaci, ya san tsibirin Pingtan gunduma ce dake fama da talauci a lardin, shi yasa da zarar ya zo tsibirin, sai ya tambaye mu cewa, ko guguwar iskar da muke gamuwa da ita tana da karfi kamar yadda take a baya, kana ya bukace mu da mu kara mai da hankali kan aikin yaki da bala'in guguwar iskar."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, ana ta shuka bishiyoyi domin rage bala'in guguwar iska a Pingtan, yanzu haka an riga an kyautata muhallin hallitu masu rai da marasa rai kamar yadda ake fata, ban da haka kuma, manyan gine-ginen more rayuwar jama'a da muhallin kasuwanci suma sun samu kyautatuwa cikin sauri. Tsohon mataimakin darektan ofishin kula da harkokin yankin gwajin tattalin arziki na Pingtan Zhuo Huabin ya waiwayi ziyarar da babban sakatare Xi ya kai a shekarar 2014, inda ya bayyana cewa, "Da zarar babban sakatare Xi ya sauka daga mota, sai ya bayyana cewa, yankin gwajin tattalin arzikin Pingtan yana da muhimmanci, ya kamata a kara maida hankali kan aikin raya yankin, kafin tashinsa a tsibirin, babban sakatare Xi ya jaddada cewa, Pingtan ya samu damar samun ci gaba mai daraja, wanda ba'a taba ganin irinsa ba a baya, abu mafi muhimmanci shi ne a kara kyautata muhallin kasuwanci a wurin, ta yadda za a jawo hankalin masu zuba jari daga sauran wurare na cikin gidan kasar Sin ko kasashen ketare."

A watan Agustan shekarar 2016, a hukumance ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince da "shirin gina tsibirin yawon bude ido na kasa da kasa a tsibirin Pingtan", daga nan tsibirin Pingtan ya kasance yanki daya kacal a kasar Sin wanda ke kokarin raya tattalin arzikinsa daga fannoni uku wadanda ke hade da gwajin tattalin arziki da ciniki maras shinge da yawon bude ido na kasa da kasa. Misali, a fannin ciniki maras shinge, an yi kirkire kirkire tun bayan kafuwarsa, misali an dauki sabbin matakai 103.

Tsibirin Pingtan wuri ne mafi kusa da tsibirin Taiwan na babban yankin kasar Sin, shi yasa yayin ziyararsa, babban sakatare Xi ya bayyana cewa, tsibirin muhimmin wuri ne da ake gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin lardunan Fujian da Taiwan, shi ma muhimmin wuri ne da ake aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen ketare na kasar Sin, yanzu haka an fara zirga-zirga kai tsaye tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan, wato idan an tashi daga Pingtan cikin jirgin ruwa, zai isa Taiwan cikin sa'o'i biyu da wani abu.

Domin jawo hankalin masu zuba jari na Taiwan, tsibirin Pingtan ya kafa wani yankin masana'antun Taiwan, ya zuwa karshen watan Agustan bana, gaba daya adadin kamfanonin da suka daddale yarjejeniyar shiga yankin masana'antun Taiwan ya kai 373, a ciki, rabinsu kamfanonin Taiwan ne. Dan kasuwar da ya zo daga lardin Taiwan Xue Qingde yana cinikin kayayyakin yau da kullum a Pingtan, ya gaya mana cewa, ya ji dadi matuka a wurin, yana mai cewa, "Na riga na yi zaman rayuwa a Pingta har shekaru da dama, gidana yana yankin gwajin tattalin arziki, kamfanina yana yankin ciniki maras shinge, da gaske ne muna jin dadi a tsibirin yawon bude ido na kasa da kasa."

Yayin ziyararsa, babban sakatare Xi ya jaddada cewa, muhallin halittu masu rai da marasa rai ya fi muhimmanci, kada a kazanta muhallanmu.

Mataimakin darektan hukumar raya aikin yawon bude ido ta Pingtan Wu Jiehua ya bayyana cewa, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, bisa bukatun babban sakatare Xi, mun kara mai da hankali kan aikin kiyaye muhalli da albarkatu, har mun samu babban sakamako yayin da muke kokarin gina tsibirin yawon shakatawa na kasa da kasa a Pingtan."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China