170921-yankin-qianhai-na-shenzhen-ya-samu-ci-gaba-cikin-sauri-a-shekaru-5-da-suka-gabata.m4a
|
Tun bayan da aka gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a shekarar 2012, kwamitin tsakiya na JKS dake karkashin jagorancin babban sakatare Xi Jinping ya sanya kokari matuka tare da daukacin al'ummun kasar domin zurfafa kwaskwarimar tattalin arziki da bude kofa ga kasashen waje, har an samu babban sakamako, yau ma bari mu yi muku bayani kan ci gaban da yankin gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin birnin Shenzhen da yankin musamman na Hongkong wajen raya aikin ba da hidima iri na zamani wato Qianhai na birnin Shenzhen na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin ya samu a cikin wadannan shekaru biyar da suka gabata.
A watan Satumban da muke ciki, tsuntsaye suna rera wakoki a lambun shan iska na dutsen Lotus na birnin Shenzhen, masu yawon shakatawa suna yawace-yawace, a tsakiyar filin dake kan dutsen, ana iya kallon mutum mutumin da aka sassaka da tagulla na marigayi Deng Xiaoping, wanda shi ne mutumin da ya tsara manufar yin kwaskwarimar tattalin arziki da bude kofa ga kasashen waje ta kasar Sin, a kusa da wurin, an ga bishiyar da babban sakataren JKS Xi Jinping ya shukka a shekarar 2012, bishiyar tana da tsayin mita uku kawai kafin shekaru biyar da suka gabata, amma yanzu ta girma har tsayinta ya kai mita goma.
A watan Disamban shekarar 2012, bayan da aka zabi Xi Jinping a matsayin babban sakataren JKS, sai ya je birnin Shenzhen yin rangadin aiki, tsohon sakataren kwamitin JKS na birnin Shenzhen mai shekaru 92 da haihuwa yanzu Li Hao ya taba raka babban sakatare Xi yayin aikin, ya gaya mana cewa, "Babban sakatare Xi yana mai da hankali sosai kan ci gaban Shenzhen, musamman ma kan yanayin da yankin Qianhai ke ciki."
Mataimakin darektan kwamitin yin kwaskwarima domin samun ci gaba na birnin Shenzhen wanda shi ne tsohon shugaban hukumar kula da harkokin yankin Qianhai Zheng Hongjie ya waiwayi ziyarar babban sakatare Xi a shekarar 2012, inda ya bayyana cewa, "Babban sakatare Xi yana fatan zai ga manyan sauye-sauye a yankin Qianhai, kuma ya ce, a yi hakuri da hangen nesa, kamar yadda ake zana hoto mai kyan gani kan takarda, ya fi kyau a dauki matakin da ya dace."
Yanzu an zabi yankin Qianhai a matsayin sabon dandalin aiwatar da manufar yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje, a saboda yankin ya sauke nauyin dake bisa wuyansa a fannoni uku, kamar su gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin Shenzhen da Hongkong, da kafa yankin gwaji na ciniki maras shinge, da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya". Zheng Hongjie yana ganin cewa, kamata ya yi a mai da hankali kan manufar da aka tsara, inda ya ce, "Shirya tsari da manufa da suka dace ya fi muhimmanci yayin da ake gudanar da kwaskwarima, misali yin kirkire-kirkire, da tsara shiri mai inganci, musamman ma wajen shigo da shahararrun kamfanoni da kwararru daga ketare."
A yankin Qianhai, an ga wani ginin wucin gadi da aka gina da tsoffin akwatunan zuba kayayyaki guda 333, ginin da ya fi jawo hankalin jama'a, an kafa ofishin hukumar kula da harkokin yankin Qianhai a cikin ginin, dalilin da ya sa haka shi ne domin ginin ya yi kusa da kamfanonin yankin, don haka cikin sauki ofishin yana iya daidaita matsalolin da kamfanonin ke fuskanta cikin gajeren lokaci.
Bayan kokarin da aka yi, yankin Qianhai ya samu babban sakamako a fannonin kirkire-kirkiren tsarin aiki, da hadin gwiwar dake tsakanin Shenzhen da Hongkong, da kafa sana'o'i da kuma gina sabbin gine-gine.
Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, adadin kamfanonin da aka kafa a yankin ya karu daga 299 a shekarar 2012 zuwa dubu 42 a karshen shekarar 2016 da ta gabata, adadin jarin waje da aka yi amfani da su ya karu daga dalar Amurka miliyan 16 a shekarar 2012 zuwa dalar Amurka biliyan 3 da miliyan 800 a bara. Ko shakka babu yanzu haka yankin Qianhai ya riga ya kasance alama ta ci gaban da aka samu wajen yin kwaskwarima a birnin Shenzhen, har ma a fadin kasar ta Sin baki daya.
Zaunannen mamban kwamitin JKS na Shenzhen wanda shi ne tsohon darektan kwamitin kula da harkokin yankin ciniki maras shinge na yankunan Qianhai da Shekou Tian Fu ya yi mana bayani cewa, "Bisa bukatar da babban sakatare Xi Jinping ya yi mana, mun riga mun samu manyan sauye-sauye a cikin shekaru biyar da suka gabata, adadin GDP na yankinmu a bana zai zarta yuan biliyan 200, nan gaba yankin zai ci gaba da taka rawa kan aikin raya kasar ta Sin."(Jamila)