Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan ga taron manema labarai, ya ce kasashen Iran, Amurka, Burtaniya, Sin, Rasha, Faransa da Jamus za su gana a hedkwatar MDD, inda ake saran za su tattauna yadda za a aiwatar da matakan da aka cimma(JCPOA) kana su ba da jagoranci a siyasance kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma game da nukiliyar kasar ta Iran.(Ibrahim)