Kwanan baya, hukumar kula da muhallin halittu ta MDD da wasu hukumomin kasa da kasa tare da hadin gwiwar kamfanin hayar kekuna na kasar Sin mai suna Mobike, suka tsaida ranar 17 ga watan Satumba ta ko wace shekara a matsayin ranar hawan keke ta duniya, a wani mataki na karfafawa jama'a gwiwar hawan keke. A hakika, a cikin shekaru biyu da suka wuce, kekunan haya sun yi ta samun karbuwa a biranen kasar Sin. A kasance tare da mu cikin shiri domin jin karin bayani.(Lubabatu)
170922-kekunan-haya-a-kasar-sin-lubabatu.m4a
|