in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana fatan bangarorin da abin ya shafa za su goyi bayan musaya tsakanin DPRK da ROK
2017-09-18 19:46:56 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, kasarsa na fatan ganin bangarorin da abin ya shafa, za su fahimta su kuma mutunta muradun jama'a, a hannu guda kuma su goyi bayan yin musaya tsakanin kasashen Koriya da Kudu ta takwawarta ta arewa

Kalaman nasa na zuwa ne bayan da shugaban kasar Koriya ta kudu Moon Jea-in ya ba da shawarar cewa, kasarsa za ta ci gaba da shirinta na kai kayayyakin agaji Koriya ta arewa, duk da takaddamar siyasar da suke ciki. Yayin da shi kuma Firaministan kasar Japan Shimzo Abe ya bukaci a samu lokacin da ya dace na kai wadannan kayayyaki.

Mr. Lu Kang ya shaidawa taron manema labarai cewa, dukkan kudurorin da kwamitin sulhu na MDD ya yanke game da kakabawa koriya ta arewan takunkumi, ciki har da sabon kudurin da kwamitin ya amince da shi mai lamba 2375, ba su da nufin yin illa ga rayuwar fararen hula da masu bukatar jin kai dake kasar.

Ya ce alummar kasashen biyu, kabilarsa daya, kuma har kullum kasar Sin tana goyon bayan kasashen biyu su karfafa yin musaya da hadin gwiwa da kuma sassantawa a tsakaninsu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China