in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar 'yan tawayen Sudan ta ce a shirye ta mai da martani ga harin da dakarun gwamnati ka iya kai mata kowane lokaci daga yanzu
2017-09-15 11:44:33 cri
Kungiyar SPLM ta 'yan tawayen Sudan, ta ce a shirye ta ke ta mai da martani ga harin da dakarun Gwamantin kasar ke niyyar kai wa yankunan dake karkashin ikonta a jihar Blue Nile.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Mubarak Ardol kakakin kungiyar na yankin arewa, tsagin Malik Agar, ya ce mayakan kungiyar sun lura dakarun Gwamnatin sun matsa daga sansaninsu dake Damazin a ranar Talata da dadaddare, inda suka tunkari wurin da mayakan kungiyar suke a yankin tsaunukan Angasana.

Sanarwar ta ce dakarun na Gwamnati, sun ci gaba da matsawa har sai da suka kai inda kungiyar ta shata daga inda kuma ake sa ran za su far musu a kowane lokaci.

Mubarak Ardol ya bayyana matakin dakarun gwamnatin a matsayin take yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin bangarorin biyu.

A watan Yulin da ya gabata ne shugaban kasar Omar al-Bashir ya tsawaita wa'adin shirin tsagaita bude wuta a dukkan yankunan da ake rikici na tsawon watanni 3 wato zuwa watan Oktoban bana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China