in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin kekunan haya na Mobike ya hada kai da MDD don kaddamar hawan keke ta duniya
2017-09-14 11:46:34 cri

Jiya Laraba, hukumar kula da muhallin halittu ta MDD da wasu hukumomin kasa da kasa tare da hadin gwiwar kamfanin hayar kekuna na kasar Sin mai suna Mobike, suka tsaida ranar 17 ga watan Satumba ta ko wace shekara a matsayin ranar hawan keke ta duniya, a wani mataki na karfafawa jama'a gwiwar hawan keke.

A 'yan shekarun da suka gabata, amfani da kekuna ya kasance wani bangare na zaman rayuwar Sinawa, wanda taimaka wajen warware matsalar cunkoson ababan hawa da ake fuskanta a tituna kasar a ko wace rana. Yanzu tsarin nan na amfani da kekunan haya yana ta samun karbuwa a wajen jama'a saboda saukin tafiya, da kiyaye muhalli.

"Game da wasu wuraren da babu motocin safa-safa da yawa da kuma jiragen karkashin kasa, amma babu nisa sosai daga wurin da mutum ya tashi zuwa inda yake son zuwa, hawan irin wadannan kekuna haya ya fi sauki, ban da araha, ana kuma iya motsa jiki."

"Ana iya samun kekunan a ko ina, don haka amfani da wadannan kekuna wata kyakkyawar hanya ce ta warware matsalar tattakin da ta bai kai nisan kilomita uku ba."

A matsayinsa na jagorar kamfanonin kekunan haya na duniya, Shugaban kamfanin kekunan haya na kasar Sin na Mobike Wang Xiao Feng ya bayyana cewa, tun bayan da Mobike ya shiga birnin Shanghai a watan Afrilu na shekarar 2016, ya zuwa yanzu, ana amfani da kekuna na Mobike cikin birane fiye da 180 na kasashe 8. Yazu kamfanin ya samar da kekuna fiye da miliyan 7, inda mutane fiye da miliyan 100 suka ci gajiyarsu.

Domin a kara fahimtar muhimmancin kiyaye muhalli, a ranar 13 ga wata, kamfanin kekunan haya na Mobike ya kula wata yarjejeniya tare da hukumar kiyaye muhalli ta MDD a nan birnin Beijing, don ayyana ranar 17 ga wata a matsayin ranar hawan keke ta duniya, inda aka yi kira da a yi kokarin rage yawan amfani da motoci, a maimakon haka a rika hawan kekuna zuwa wajen aiki ko sauran wuraren hidimomi, ta yadda za a warware matsalar cunkoso ababan hawa da gurbata muhalli. Wang Xiaofeng ya bayyana cewa,

"Muna farin ciki sosai da hadin gwiwa tare da hukumar kiyaye muhalli ta MDD da cibiyar nazarin albarkatu ta duniya, wajen ba da shawarar kaddamar da ranar hawan keke ta duniya. Muna fatan za a tuna da kekuna a duk lokacin da bukaci tuka mota, ko shirin yin wata gajeriyar tafiya. Wannan shi ne burin da muke fatan cimmawa tare da kokarin kowa da kowa."

A ganin mataimakin babban sakataren MDD kuma shugaban zartaswa na hukumar kiyaye muhalli ta majalisar Erik Solheim, yanzu yanayin hazo ya riga ya zama wata babbar matsalar da ke yin illa ga lafiyar mutane da kuma kawo mummunan tasiri ga zamanmu. Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, a cikin dalilan da suka haddasa tsanantar yanayin hazo, iska mai gurbata muhalli da motoci ke fitarwa,suna daga cikin manyan matsaloli, amma amfani da kekuna na iya kiyaye muhallinmu sosai. Mr. Solheim yana mai cewa,

"yau kusan shekaru biyu da suka gabata ke nan, ba mu taba sanin tsarin kekunan haya ba, lallai wannan wani sabon abu ne mai muhimmanci. Ban da wannan kuma, kamfanin Mobike da sauran kamfanonin kekunan haya suna amfani da wasu fasahohin sadarwa don samar mana kekuna masu yawa. Sakamakon amfani da na'urar GPS, kana iya gano kekuna mafi kusa da kai, kuma kana iya ajiye su a duk inda kake so bayan ka biya bukatunka. Shawarar da muka bayar a yau wata shawarar ce ta kiyaye muhalli, don haka muna farin ciki sosai, sabo da mun samu wata hanyar warware matsalar gurbata muhalli yanzu."

Bisa rahoton cibiyar bayani ta kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa watan Yuli na bana, yawan kekunan haya da jama'a ke iya amfani da su ya kai kimanin miliyan 16 a cikin kasar Sin, wanda ya samar da guraban aikin yi ga mutane dubu 100. Yanzu mutanen da ke amfani da kekunan ya zarce miliyan 106, wanda ya kai kashi 14.11 cikin dari na dukkan mutanen da ke amfani da Intanet.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China