in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane 500 ne zabtarewar laka ta shafa a kudu maso yammacin kasar Rasha
2017-09-01 21:03:05 cri
Sama da mutane 500 ciki hadda baki 'yan kasashen waje sama da 130, daga kasashe 10 ne zabtarewar laka ta yiwa shinge, a yankin Kabardino-Balkaria dake kudu maso yammacin kasar Rasha.

Kafofin watsa labaran kasar sun rawaito hukumomin bada agajin jin kai na tabbatar da aukuwar wannan ibtila'i. Rahotanni sun kara da cewa, baya ga gidajen mazauna yankin, wasu 'yan yawon bude ido 350, da suka yi rajista da kamfanonin bada hidima 49, a sansanonin masu yawon shakatawa 27, ciki hadda baki da dama sun gaza fita daga yankin.

An ce shimilin lakar ya gangaro ne daga tsaunin Adyl-Su, ya kuma rufe dukkanin hanyoyin fita daga wannan yankin. To sai dai kuma yanzu haka ana daukar matakan ganin an ceto wadanda wannan lamari ya rutsa da su lami lafiya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China