Tun daga sanyin safiyar wannan rana, maniyyatan sanye da fararen kaya suka tashi zuwa Mina da ke da tazarar kilimita bakwai daga babban masallacin Makka. Nan da kwanaki biyar masu zuwa, maniyyata daga sassa daban daban na duniya za su gudanar da ayyukan addini a Makka da ma sauran wasu wurare uku dake dab da shi.
Gwamnatin Saudiyya ta tsaurara matakan tsaron maniyyata, inda ta jibge sojoji kimanin dubu 100 da ma'aikatan kashe gobara sama da dubu uku da kuma motocin kashe gobara dari biyar don zama cikin shirin ko ta kwana a sassan da ake aikin hajji.(Lubabatu)