in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoto: Gina yankin masana'antu wani muhimmin bangare na hadin gwiwar Sin da Afirka
2017-08-30 10:48:24 cri
A jiya Laraba ne a nan birnin Beijing cibiyar nazarin harkokin yammacin Asiya da Afirka ta kwalejin nazarin kimiyyar zamantakewar al'umma ta kasar Sin tare da hadin gwiwar madaba'ar wallafa littattafan ilmin zamantakewar al'umma da kimiyya suka kaddamar da rahoton ci gaban nahiyar Afirka daga shekarar 2016 zuwa 2017.

Rahoton ya yi nuni da cewa, yayin da aka shiga karni na 21, kasashen Afirka sun kara himmatuwa wajen bunkasa masana'antu, musamman ma gina yankin masana'antu. Duk da wannan ci gaba da aka samu, akasarin kasashen Afirka ba za su iya dogara da kansu ba, a don haka suna bukatar hadin gwiwa da sauran kasashen duniya ta fannonin tara kudaden jari da shigo da fasahohin zamani da yadda ake tafiyar da yankin masana'antu, al'amarin da ya samar da damar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Rahoton ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, yawan yankunan masana'antu da kasar Sin ta gina ko kuma take ginawa ko shirin ginawa a kasashen Afirka ya kai kusan 100, kuma tuni aka fara aiki da 30 daga cikinsu. Gina yankin masana'antu ya dace da shawarar da kasar Sin ta gabatar ta ziri daya da hanya daya da kuma ajandar raya nahiyar Afirka nan da 2063. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China