An dai gabatar da rahoton ne domin nazari, a yayin taron kwanaki 5 da kwamitin majalissar wakilan jama'ar kasar Sin NPC ke gudanarwa a watanni biyu biyu, taron da a wannan karo aka bude a ranar Litinin.
Rahotan ya shaida cewa, kasar Sin ta ayyana shekarar 2020, a matsayin wa'adin kammala gina al'umma mai wadata, matakin da ba zai tabbata ba har sai an cimma nasarar yaki da fatara.
Domin cimma wannan manufa, an bayyana cewa, Sin na bukatar fidda mutane miliyan 10 duk shekara daga kangin talauci, adadin dake nufi fitar da mutum miliyan daya duk wata, ko mutum guda 20 duk minti daya daga kangin talauci tsakanin al'ummar Sinawa. (Saminu Alhassan)