in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka rasu sakamakon zaftarewar kasa a kudu maso yammacin Sin ya karu zuwa 17
2017-08-29 20:37:24 cri
Yawan mutanen da suka rasu, sakamakon zaftarewar kasa da ta auku, a gundumar Nayong dake lardin Guizhou a kudu maso yammacin Sin da safiyar jiya Litinin ya karu zuwa mutum 17.

Kaza lika har yanzu ba a kai ga gano wasu mutane 18 da suka bace sakamakon aukuwar ibtila'in ba.

Ya zuwa karfe 4:30 na yammacin yau Talata an gano mutane 25, ciki hadda 17 da suka riga mu gidan gaskiya, da wasu 8 da suka jikkata wadanda kuma tuni aka garzaya da su asibiti domin samun jiyya.

Sassan mahukunta masu lura da aukuwar lamarin dai sun ware kudi har Yuan miliyan 2.5, kwatankwacin dalar Amurka 379,100 a matsayin kudaden tallafi ga yankin. Kaza lika an aike da tantuna, da da shinfidu, da abinci zuwa yankin.

Bisa jimilla, adadin mutanen da suka rasa matsuguni, wadanda kuma aka fidda su zuwa tudun mun tsira sakamakon aukuwar wannan bala'i, sun kai mutum 195 daga iyalai 66.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China