Hua Chunying ta ce Sin na fatan kasashen biyu, za su martaba manufofin tsaro da suka jibanci Sin da sauran kasashe dake yankin zirin koriya. Jami'ar ta yi wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai da aka gudanar a yau, gabanin taron manyan jami'an tsaron kasashen na Amurka da koriya ta kudu a gobe Laraba.
Ta ce na'urorin THAAD ba za su magance kalubalen da kasashen wannan yanki na zirin koriya ke fuskanta ba. Maimakon haka matakin zai kara dagula yanayi ne kawai. Kaza lika hakan na iya gurgunta tsaron yankin baki daya ciki hadda Sin, tare da tsananta halin da ake ciki a zirin na Koriya.