A shekarar 2015, an bayar da wani hoto game da wani karamin yaro mai suna Aylan Kurdi na kasar Syria da aka gano a bakin tekun kasar Turkiya, wanda ya nutse a cikin ruwa, ya sanya duk duniya baki daya mamaki kwarai da gaske, lamarin ma ya nuna cewa, ana samun tabarebarewar yanayin jin kai a kasar ta Syria. To sai dai, a yayin da ake fuskantar wannan matsalar 'yan gudun hijira ta duniya, wane irin ayyuka ne ya kamata a yi don shawo kan matsalar? Kuma yaya za a yi don tallafawa wadannan 'yan gudun hijira, musamman ma yara? Wadannan su ne batutuwa biyu da kasashen duniya ke tunani a kai.
Kwanan baya, wakilan rediyon mu na CRI sun kai ziyara ga wani shiri mai taken "Makomar bai daya", na cibiyar inganta dokokin kasa da kasa wato CIIL a takaice, inda suka gamu da wasu masu aikin jin kai da suka fito daga kasar Sin. Masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu duba yadda wadannan 'yan mata guda 7 suka tallafawa wasu 'yan gudun hijira kananan yara na kasar Syria.
170828-Masu-aikin-jin-kai-sun-nuna-kauna-tare-kuma-da-yin-rakiyar-yan-gudun-hujira-yara-na-kasar-Syria-Bilkisu.m4a
|