in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taro tsakanin kasashen BRICS kan yadda za su tafiyar da harkokin mulki
2017-08-18 13:58:44 cri

An kaddamar da wani taron karawa juna sani a jiya Alhamis, tsakanin kasashen BRICS game da yadda za su tafiyar da harkokin mulkin kasa a birnin Quanzhou na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin. Wasu jami'an gwamnati da kwararru da masana daga kasashen Sin, da Rasha, da Brazil, da Indiya, da Afirka ta Kudu, da Tanzaniya, da Chile da Mexico sun hallara, inda suka yi musayar ra'ayoyi dangane da yadda za'a karfafa hadin-gwiwa don neman ci gaba kafada da kafada.

Babban taken taron karawa juna sanin a wannan karo shi ne, budewa juna kofa, da neman cimma moriya tare. Mataimakin shugaban sashen yayyata ayyukan kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Mista Huang Kunming, ya gabatar da jawabi, inda ya ce, shugabannin kasashe membobin kungiyar BRICS sun cimma matsaya cewa, za su yi musayar ra'ayi kan yadda za su tafiyar da harkokin mulkin kasa, kana, wannan taron da aka yi, wani muhimmin sashi ne na ganawar da za'a yi tsakanin shugabannin kasashen BRICS a birnin Xiamen na kasar Sin a watan Satumban bana.

Mista Huang ya ce:

"Kwalliya ta biya kudin sabulu ta fuskar hadin-gwiwar kasashe membobin kungiyar BRICS, abun dake kunshe da bangarori da fannoni daban-daban. Kasashen biyar dake kungiyar BRICS na kara yin hadin-gwiwa da mu'amala tsakaninsu. Bugu da kari, kasashen BRICS sun lalubo hanyoyin da za su bi wajen tafiyar da harkokin mulki da neman ci gaba, wadanda ke dacewa da hakikanin halin da ake ciki a wadannan kasashe."

Sakamakon bunkasa da ci gaban da kasar ta samu, akwai kasashe da dama wadanda ke son koyon dabarun gwamnatin kasar Sin na tafiyar da harkokin mulkin kasa. Robert Lawrence Kuhn shi ne fitaccen masani daga kasar Amurka, kana kwararre kan harkokin kasar Sin, wanda ya bayyana cewa, salon tafiyar da mulkin kasa da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bullo da shi, zai iya zama abun misali ga kasashen BRICS da ma sauran kasashen duniya. Mista Kuhn ya ce:

"Shugaba Xi Jinping ya yi alkawari ga duk fadin duniya cewa, kasar Sin za ta kara nuna himma da kwazo wajen tafiyar da harkokin duniya, da daukar kwararan matakai ta fuskar shimfida zaman lafiya da neman bunkasa a fadin duniya, Wannan abu yana da ma'ana sosai. Irin dabarun da gwamnatin kasar Sin take da su ta fannin tafiyar da harkokin mulki, za su iya taimakawa sauran kasashen duniya."

Har wa yau kuma, a wajen taron karawa juna sanin da aka yi wannan karo, mahalarta taron sun tofa albarkacin bakinsu kan yadda za'a kara kyautata tsarin kungiyar BRICS. A nasa bangaren, shugaban rukunin majalisun dokokin Indiya da Sin, Tarun Vijay ya ce, BRICS ba kawai kungiyar gamayya ba ce, wani babban iyali ne. Yawan tattalin arziki na kasashe membobin BRICS ya kai kashi 22.5 bisa dari na yawan tattalin arzikin duk fadin duniya, har ma yawan kudin cinikayya na wadannan kasashe biyar ya kai kashi 17.2 bisa dari na yawan kudin cinikayya na duk duniya. Duk da cewa kasashe biyar dake cikin kungiyar BRICS suna da mabambantan hanyoyin da suke bi wajen neman samun bunkasuwa da ci gaba, suna hada karfi sosai da sosai. Tarun Vijay ya bayyana ra'ayinsa game da makomar tsarin kungiyar BRICS, inda ya ce: "Hannu daya ba ya daukar jinka. Ya kamata mu yi kokarin cimma burinmu tare, da neman samun ci gaba kafada da kafada."

Shugaban cibiyar nazarin huldar kasa da kasa na zamani ta kasar Sin, Mista Ji Zhiye na ganin cewa, kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin hadin-gwiwar kasashen kungiyar BRICS, kuma ana sa ran za'a cimma muhimman nasarori a wajen ganawar shugabannin kasashen BRICS wadda za a yi a watan Satumba a birnin Xiamen na lardin Fujian dake kasar Sin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China