170823-An-kaddamar-da-cibiyar-nazarin-harkokin-Najeriya-a-jamiar-horas-da-dalibai-ta-Zhejiang.m4a
|
Cibiyar wadda ita ce irinta ta farko tsakanin jami'o'in kasar Sin za ta mayar da hankali ne wajen nazartar fannoni Ilimi, al'adu, kabilun Najeriya, addinai da hadin gwiwar Sin da Najeriya. A daya hannun kuma, taron karawa juna sanin da aka gudanar yayin kaddamar da wannan cibiya ya samu halartar wakilan kamfanonin kasar Sin dake Najeriya da wakilin rundunar sojojin kasar Sin da dalibai daga bangarorin biyu dake nazarin harkokin Afirka da Najeriya.
Taron ya kuma tattauna a kan batutuwan tsaro, zuba jari da cinikayya tsakanin sassan biyu, da kuma matakan kare kadarorin da sassan biyu suka zuba jari a kasashen juna.
Masana na kallon kafa cibiyar a matsayin wani muhimmin mataki da zai karfafa hadin gwiwar Sin da Najeriya daga dukkan fannoni. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)