170816-Aikin-jigilar-alhazai-a-nan-kasar-Sin.m4a
|
A nan kasar Sin dake da miliyoyin musulmai kamar sauran kasashe da mutanensu suke zuwa aikin hajji, ta kan shiryawa alhazanta jirage da masaukai da tawagar likitoci da masu dafa abinci da sauran ma'aikata masu yi musu hidima tun daga nan gida har zuwa kasar Saudiya da kuma dawowa gida.
Baya ga maniyata dake zuwa aikin hajji karkashin hukuma, akwai kuma masu zuwa ta jirgin yawo ko kamfanoni masu zaman kansu.
Sai dai duk da kasancewar hukumomin kula da harkokin alhazai da kasashe ke kafawa da nufin saukaka ayyukan hajji ga al'ummominsu a wasu kasashen hakan ba ya samu ba.
Yayin da sauran maniyata daga sassan duniya ke haramar sauke aikin Ibada, su ma maniyatan Sin kimanin sama da 12,000 ne ake sa ran za su halarci aikin hajjin na bana kuma sun fara tashi daga sassan kasar Sin daban-daban.
Masu sharhi na ganin cewa, wajibi ne kasashe su fito da tsare-tsare da suka dace don kaucewa irin matsaloli da wahalhalu da maniyatta ke fuskanta a shirye-shiryen tafiya aikin hajji da kuma lokacin da alhazai ke kasa mai tsarki har zuwa lokacin dawo wa gida bayan kammala aikin Ibada. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)