Yau Laraba da yamma, mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya gana da mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin kuma gwamnan babban bankin kasar Mista Zhou Xiaochuan a Beijing. Mai martaba sarkin Kano ya ce, yana fatan ganin karin kamfanonin kasar Sin su je Kano, su zuba jari a fannonin kere-kere, mulmula karafa, sarrafa takalma, saka tufafi da makamantansu.(Murtala Zhang)