in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani babban kusan kungiyar Al-shabaab ya mika wuya
2017-08-16 13:07:05 cri
Babban kwamanda na biyu na kungiyar Al-Shabaab mai tsattsauran ra'ayi Mukhtar Robow a jiya Talata ya sanar da fita daga kungiyar, tare da mika wuya ga gwamnatin Somaliya.

A taron manema labarai da aka kira a wannan rana a birnin Mogadishu, babban birnin kasar, Mukhtar Robow ya ce, yana fama da sabanin ra'ayi da sauran kusoshin kungiyar ta Al-Shabaab, kuma yana ganin cewa, abubuwan da kungiyar ke gudanarwa yanzu ba su dace da muradun jama'ar Somaliya ba, don haka, ya yanke shawarar fita kwata-kwata daga kungiyar. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China