Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Ⅱ, na ci gaba da ziyarar aiki a birnin Shenzhen na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, kuma da safiyar yau Asabar ne ya ziyarci babban dakin adana kayan tarihi na birnin Shenzhen, inda ya ganewa idansa manyan nasarori da ci gaban da Shenzhen ta samu, musamman bayan kasar Sin ta fara aiwatar da muhimmiyar manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekara ta 1978.