170811-mai-martaba-sarkin-kano-na-ci-gaba-da-ziyara-kasar-Sin-murtala.m4a
|
Yau Jumma'a ce rana ta biyu, da mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ke ci gaba da ziyara a nan kasar Sin, inda ya bar birnin Guangzhou ya zuwa birnin Shenzhen dake lardin Guangdong don ci gaba da rangadi. A yau, tawagar mai martaba sarkin Kano ta ziyarci shahararren kamfanin sadarwa na kasar Sin Huawei, gami da yankin cinikayya maras shinge mai suna Qianhai dake birnin Shenzhen. Wakilinmu Murtala Zhang ya samu damar zantawa da mai martaba sarkin. Ga kuma yadda ta kasance.