in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Idon kiyaye gandun daji a filin itatuwa na Saihanba
2017-08-07 13:24:08 cri


Kandagarkin abkuwar gobara, yana gaba da komai a duk inda ake da wani filin dashe na itatuwa. Yanzu haka ko da yake ana amfani da wasu hanyoyin zamani wajen sa ido kan abkuwar gobara a filin itatuwa na Saihanba da ke lardin Heibei na kasar Sin, amma kasancewar aikin na da matukar muhimmanci ya sa masu sa ido kan abkuwar gobara da ke aiki a hasumiyar hangen nesa suka zamo tamkar idanun gandun dajin wajen kandagarkin abkuwar gobara.

Abokiyar aikinmu Tasallah Yuan dauke da karin bayani, dangane da wadannan masu sa ido.

Liu Jun, mai shekaru 46 da haihuwa, yana aikin sa ido kan abkuwar gobara a filin itatuwa na Saihanba. Yayin tattaunawar mu da shi, da zarar mun ambato gandun daji mai fadin murabba'in kilomita gomai da ke kewayensa, sai ya nuna mana gandun dajin daga taga, tare da bayyana mana sunayen wurare da dama daidai kuma cikin sauri. Ko da gandun daji da muka hanga daga tagar, gandun daji ne mai launin kore wanda ba mu iya bambance shi da gandun daji da ke sauran wurare ba.

Liu Jun ya tsara wata taswira a kwakwalwarsa, kuma idanunsa sun fi saura iyawar gani. Dansa Liu Zhigang, wanda yake koyon yadda za a sa ido kan abkuwar gobara, ya nuna babban yabo kan kwarewar mahaifinsa. Liu Zhigang ya gaya mana wani labarin mahaifinsa."Wata rana, ana rana sosai, yayin da muke tafiya cikin mota, sai rairayi da hayaki suka turnuke. Na yi tsammanin gobara ce ta tashi, sai na gaya wa mahaifi na, akwai hayaki! Mu gudu, kana gani ko! Mahaifina ya hanga nesa ya ce, a'a, rairayi ne kawai. Ba matsala! Mota ce ta ta da shi."

A filin itatuwa na Saihanba, kowa ya yaba wa masu sa ido kan abkuwar gobara da ke aiki a hasumiyar hanga. Saboda da farko, aikinsu yana da matukar muhimmanci. Na biyu kuma, a kan gina hasumiyar hanga a wurare masu tsayi, wadanda suka yi nisa da wuraren da ake samun yawan mutane. Dole ne masu sa idon su jure wahalar jin kadaici shekara da shekaru.

A shekarar 2006, Liu Jun da matarsa Qi Shuyan sun fara aikin sa ido kan hasumiyar hange mafi tsayi a filin itatuwa na Saihanba. A ganin Liu Jun, ya koma wurin da mahaifansa suka taba aiki a baya.

Yanzu shekaru 11 ke nan da Liu Jun da matarsa suka dauka suna aikin sa ido kan abkuwar gobara. A cikin wa'adin yin rigakafin abkuwar gobara na tsawon watanni 6 a ko wace shekara, dole ne su mika rahoto a ko wadanne mintoci 15 a rana, yayin da suka mika rahoto a ko wace awa a dare a wasu muhimman lokuta. Ko da yake aikinsu yana da wahala sosai, amma Liu Jun da matarsa suna taimaka wa juna sosai.

Aikinsu mai matukar wahala da kuma wurin zama maras kyau da suke kasancewa sun sanya ga alama Liu Jun da matarsa Qi Shuyan wadanda shekarunsu suka wuce 40 kawai da haihuwa su fi takwarorinsu tsufa. Amma duk da haka, sun nuna gamsuwa sosai kan aikinsu da kuma zaman rayuwarsu a yanzu. Kuma babban burinsu shi ne za a ci gaba da kiyaye gandun dajinsu yadda ya kamata bayan da suka yi ritaya. Liu Jun ya ce,"Mun shirya kare gandun dajin nan har ritayar mu. Za mu mika gandun dajinmu a hannun masu gadonmu. Wannan shi ne babban burinmu."

Dansu Liu Zhigang ya fahimci burin mahaifansa sosai. Ya yi watsi da aikinsa a birnin Shanghai, ya koma gida, ya fara aikinsa na wucin gadi a matsayin mai kashe gobara. Ya kan koma hasumiyar hange da mahaifansa suke aiki a ciki, ya yi koyi daga wajen mahaifinsa. Ya yi fatan cewa, zai gaje su bayan sun yi ritaya.

Amma da farko Liu Jun bai yarda da shi ba, saboda a ganinsa, dansa Liu Zhigang, sabon hannu ne kawai, ba zai iya kare gandun dajinsa ba. Amma a karshe dai, Liu Zhigang ya shawo kan mahaifinsa bisa hakikanin matakan da ya dauka. Sa'an nan amaryarsa ita ma tana mara masa baya sosai.

Ko da yake yanzu kwarewar Liu Zhigang wajen sa ido kan abkuwar gobara ba ta kai ta mahaifinsa ba tukuna. Amma sannu a hankali ya san wasu fasahohi. Liu Jun ya yi fatan cewa, dansa Liu Zhigang zai gaje shi, zai ci gaba da kiyaye gandun daji, wanda yake kare shi da zuciya daya."Mahaifinsa da takwaransa sun gina wannan filin itatuwa, sun mika filin itatuwan a hannunmu, za mu mika filin itatuwan a hannun wasu. Ana gadar filin itatuwan daga zuriya zuwa zuriya. Dole ne mu kiyaye filin itatuwan yadda ya kamata." (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China