170804-an-dasa-itatuwa-da-samun-bunkasuwa-ba-tare-da-gurbata-yanayi-ba-a-sahanba-zainab.m4a
|
Ma'anar Sahanba ita ce wuri mai girma da kyaun gani. Yanayin zafi shi ne yanayin da ya fi dacewa da Sahanba, kuma ya jawo masu yawon shakatawa da dama zuwa wurin.
Dalilin da ya sa wurin yake da kyaun gani shi ne saboda itatuwa masu tarin yawa dake wurin, wadanda suka kawata yanayin wurin. Bisa binciken da kwalejin kimiyyar ilmin kula da daji ta kasar Sin ta yi, muraba'in filin da aka dasa itatuwa a Sahanba ya kai eka dubu 74.7, kana dajin yana iya daukar ruwa tare da tsabtace ruwan da ya kai kyubik mita miliyan 137, haka yawan iskar Oxygen da wurin ya samar yana iya biya bukatun numfashin mutane miliyan 2 har na tsawon shekara daya.
A shekarar 1962 ne, gwamnatin kasar Sin ta kafa filin itatuwa a Sahanba, a kan samu saukar dusar kankara har na tsawon watanni 7 a ko wace shekara, kana sanyin wurin a lokacin hunturu ya kai kasa da ma'aunin Celcius 43. Saboda yanayin wuri, an tura wani rukunin dasa itatuwa dake kunshe da mutane 369 wadanda matsakaicin shekarunsu bai kai 24 ba. Ban da matsalar sanyi da saukar dusar kankara, wata matsalar ta daban da rukunin ke fuskanta ita ce kasa da kashi 8 cikin dari kawai na itatuwan da suka dasa a farkon shekaru biyu bayan kafuwar rukunin aka iya kiyayewa, duk ragowar sun mutu. Shugaban ofishin ilmin kula da daji na filin itatuwa na Sahanba Cheng Shun ya bayyana cewa,
"Matakin farko da aka dauka bayan kafa filin itatuwan, shi ne an shiga da itatuwa daga wasu sassa, amma ba mu iya kiyaye su ba. Yana da wuya da shigo da itatuwa daga waje, kana akwai fannoni daban daban yayin da ake dasa itatuwa, idan har ba a gudanar ko wane fanni yadda ya kamata ba, ba za a dasa itatuwan yadda ya kamata ba."
Ko da matsalolin da ke gabansu, amma mazauna filin Sahanba sun warware matsalolin shigowa tare da dasa itatuwa a wurin, ta hanyar yin amfani da kimiyya wajen gudanar da aiki da yin kirkire-kirkire, har ma wasu fasahohin da suka samu sun zama irinsu na farko a fannin ilmin kula da daji a duniya.
Bayan da aka dasa itatuwa, mazauna filin Sahanba suna tunanin yadda za a yi amfani da daji a harkokin rayuwar yau da kullum. A ganinsu, akwai bukatar yin amfani da albarkatun daji mai dorewa. Mataimakin shugaban filin itatuwa na Sahanba Chen Zhiqing ya bayyana cewa,
"Abu mafi muhimmanci wajen gudanar da aiki shi ne kiyaye daji da kuma muhalli. Ya kamata a gudanar da dukkan ayyuka yadda ya kamata da yadda zai dace da halin da ake ciki, maimakon samun moriya kawai. Ya kamata a gudanar da ayyuka don samun ci gaba mai dorewa ta hanyar kiyaye muhalli."
Tun shekarar 2012, aka fara daukar matakan rage sare itatuwa dake filin itatuwa na Sahanba. A waje daya kuma, an kokarta wajen bunkasa sha'anin dasa itatuwa, da na yawon shakatawa, da samar da wutar lantarki bisa karfin iska. Bayan wasu shekaru kuma, an kyautata tsarin bunkasuwar tattalin arziki a wurin zuwa tsarin samun ci gaba ba tare da gurtaba yanayi ba.
Tun daga shekarar 2013, an fara gina kayayyakin more rayuwa a wurin, an kuma kafa tsarin samar da ruwa, da wutar lantarki, da internet, da gina hanyoyin motoci a wurin. Shugaban filin itatuwa na Sahanba Liu Haiying ya bayyana cewa, yayin da ake samun ci gaba ba tare da gurtaba muhalli ba a wurin, matakin ya taimaka ga samun bunkasuwar tattalin arziki a dukkan yanki gaba daya. Liu Haiying ya kara da cewa,
"Mazauna yankin suna iya samun guraben aikin yi yayin da filin itatuwa ke da bukatar daukar ma'aikata, wannan wata dama ce gare su wajen samun kudin shiga kai tsaye. Haka kuma, mazauna wurin suna iya cin gajiyar amfanin dake daji. Bugu da kari, suna iya raya wasu ayyukan da ke da nasaba da sha'anin yawon shakatawa. Haka zakila ma, ganin yadda filin itatuwa na Sahanba ya yi wajen dasa itatuwa, suna iya koyon fasahohin dasa itatuwa, sa'an nan su sayar da tsiron dashe su samu kudi."
Alkaluman kididdiga na nuna cewa, a kowace shekara, yawan kudin shiga da filin itatuwa na Sahanba yake samarwa yankin da kewayensa ya kai Yuan fiye da miliyan 600. (Zainab)