in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya zartas da kudurin hana kungiyoyin 'yan ta'adda mallakar makamai
2017-08-03 13:42:10 cri

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani taro jiya Laraba, inda aka zartas da wani kuduri dake son ganin an hana kungiyoyin 'yan ta'adda samun makamai, tare da bukatar kasashen duniya su karfafa hadin-gwiwa, domin katse hanyoyin da kungiyoyin 'yan ta'adda suka bi wajen samun makamai, a wani mataki na kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya.

Darektan gudanarwa na ofishin yaki da miyagun kwayoyi da manyan laifuffuka na Majalisar Dinkin Duniya Yury Fedotov, da darektan cibiyar yaki da ta'addanci ta MDD Jehangir Khan, da mukaddashin darektan gudanarwa na kwamitin yaki da ta'addanci na kwamitin sulhun MDD Chen Weixiong, gami da wasu jami'ai ne suka halarci taron.

Mista Yury Fedotov ya jaddada cewa, hana 'yan ta'adda samun makamai na da matukar muhimmanci ga aikin yaki da ta'addaci, inda ya ce:

"Kwamitin sulhun MDD ya san cewa, hana 'yan ta'adda su samu makamai, ciki har da makaman kare dangi, na da muhimmancin gaske ga ayyukan murkushe ayyukan ta'addanci. 'Yan ta'adda suna samun makamai ta hanyoyi da dama a fadin duniya, ciki har da kwace wasu makaman da ba'a adana su yadda ya kamata ba. Kana 'yan ta'addan suna yi amfani da yanar gizo ta Intanet domin jigilar makamai, abun da ya kara haifar da barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya."

A jawabinsa mukaddashin darektan gudanarwa na kwamitin yaki da ta'addanci na kwamitin sulhun MDD Mista Chen Weixiong ya bayyana cewa, ana fuskantar kalubale da dama a halin yanzu, a kokarin hana 'yan ta'adda su samu makamai, kana ana bukatar kara kokari a wannan fanni. Mista Chen ya ce:

"Duk da cewa kasashe membobin kwamitin sulhun MDD sun samu ci gaba a fannin hana 'yan ta'adda mallakar makamai, amma akwai sauran rina a kaba dangane da wannan batu. Ya kamata a duba gami da inganta dokokin da aka kafa game da yaki da kasashen dake samar da makamai ga 'yan ta'adda, da kara sa ido kan mutanen dake mallaka ko kuma yin amfani da makamai, da kuma tabbatar da cewa, an adana makaman da sojoji ko dakaru suke amfani da su yadda ya kamata, ta yadda makaman ba za su yadu zuwa wuraren da ake fama da rikice-rikice ba. Har wa yau, ya zama dole a samar da horo na musamman da na'urori gami da kayan aiki na zamani ga kasashe da dama, domin aiwatar da kudurin kwamitin sulhun MDD dangane da hana jigilar makamai, tare kuma da fadada hadin-gwiwa tsakanin MDD da kungiyoyi gami da kasashe daban-daban."

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD, Mista Liu Jieyi, shi ma ya yi maraba da sabon kudurin yaki da ayyukan ta'addanci da aka zartas a yayin taron kwamitin sulhun, inda ya ce, ya kamata kasashen duniya su bullo da ma'auni guda, domin toshe hanyoyin da kungiyoyin 'yan ta'adda suke bi wajen mallakar makamai. Mista Liu ya ce:

"Kudurin kwamitin sulhun MDD ya bukaci dukkanin kasashe da kada su samar da duk wani tallafi ga kungiyoyin 'yan ta'adda, ciki har da tallafin makamai. Ya zama tilas kasashen duniya su aiwatar da kudurin da kwamitin sulhun ya amince da shi. Hanya daya ta hana kungiyoyin 'yan ta'adda mallaka ko jigilar makamai tsakaninsu, ita ce kawai amfani da ma'auin da MDD ta tsara, da daukar kwararan matakai tare. Kuma yin hakan zai sa kungiyoyin 'yan ta'adda ba za su iya aikata ayyukan ta'addanci ba."

Mista Liu Jieyi ya kuma jaddada cewa, ya kamata kasashe membobin MDD su karfafa hadin-gwiwa ta fuskar yaki da ayyukan ta'addanci, musamman hana 'yan ta'adda samun makamai. Mista Liu ya ce:

"Ya kamata kasashe daban-daban su yi kokarin musanyar bayanai dangane da yadda kungiyoyin 'yan ta'adda za su samu makamai, da yin koyi da juna, game da yadda za'a yaki yadda ake sayar da makamai da kera su ba bisa doka ba."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China