Wadannan ka'idojin da aka fitar na kunshe da kudurori na zahiri, bisa tsari na kimiyya, da ingantattun manufofin gudanarwa, da sanya ido, wadanda za su dace da manufofin kasar nan da shekarar 2020.
Sauran fannonin da matakan suka shafa, sun hada da batun kara yawan asibitoci, da inganta wadanda ke yankunan karkarar kasar, da horas da ma'aikatan lafiya ta yadda za su dace da zamani, da kuma baiwa sassa masu zaman kansu daga ketare izinin kafa asibitoci kamar yadda doka ta tanada.
Masu fashin baki na fatan sabbin ka'idojin raya ayyukan kula da lafiyar al'ummar Sinawan, za su mai da hankali ga tabbatar da nasarar kare lafiyar al'umma baki daya, da tabbatar da cewa, asibitoci na aiki ba tare da mai da hankali ga neman riba ba, tare da cikakken tsarin gudanarwa na zamani.
Masana na ganin cewa, wannan mataki da gwamnatin kasar Sin ta dauka, yana kara tabbatar da kudurin mahukuntan kasar game da kokarin da suke na tabbatar da lafiya al'umma ta yadda zai dace da yanayin da ake ciki. A hannu guda ana fatan su ma jama'a za su ba da tasu gudummawar yayin da gwamnati ke kokarin sauke nauyin dake kanta na inganta lafiyar al'ummointa. (Saminu, Ahmed, Ibrahim/Sanusi Chen)
170809-Gwamnatin-kasar-Sin-ta-bullo-da-matakan-kula-da-asibitoci-a-kasar.m4a
|