in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ingiza gyare-gyaren soja
2017-08-02 14:04:44 cri

A cikin shekaru 90 da suka wuce tun bayan da aka kafa rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin(PLA), ba a taba daina yi wa rundunar gyare-gyare ba.

A yayin bikin faretin soja da aka shirya don murnar cika shekaru 90 da kafa rundunar sojan 'yantar da jama'ar kasar Sin, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar kuma shugaban kwamitin soja na jam'iyyar kwaminis ta kasar ya ba da umurnin kara yiwa rundunar sojan kasar gyaran fuska ta yadda za a kasance a sahun gaba a duniya.

A ranar 3 ga watan Satumba na shekarar 2015, a yayin da aka gudanar da faretin soja a dandalin Tian'anmen da ke nan birnin Beijing domin murnar cika shekaru 70 da samun nasarar yaki da maharan kasar Japan kana da masu ra'ayin dannayi a duniya baki daya, shugaban kasar Xi Jinping ya sanar wa kasashen duniya niyyar kasar Sin ta wanzar da zaman lafiya a duniya da kuma raya rundunar soja tare da yi mata gyare-gyare. "Ina sanar da duniya cewa, kasar Sin za ta rage sojoji dubu 300 cikin sojojin da take da su."

Wannan shi ne mafarin aikin yi wa rundunar sojan kasar gyare-gyare, gyare-gyaren da za su shafi makomar rundunar sojan kasar, wadanda kuma suka kasance gyare-gyare da aka yi wa rundunar karo na 13 tun bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949.

A game da sabbin gyare-gyaren da ake gudanarwa, mataimakin shugaban ofishin kula da harkokin gyare-gyare da tsare-tsare na rundunar sojojin kasar Mr.He Renxue ya ce, "Gyare-gyaren da muke yi ba kananan gyare-gyare ko kuma gyare-gyare a wasu sassa kawai ba ne, amma manyan gyare-gyare ne da ya shafi dukkanin fannonin soja baki daya, wadanda suka sha banban da gyare-gyaren da aka gudanar a tarihin rundunar, haka kuma sun sha bamban da gyare-gyaren da rundunonin soja na sauran kasashen duniya suka gudanar, don haka, ba za mu iya misalin abin da muka koya, lamarin kuma da ke da matukar wahala."

A game da gyare-gyaren, masani ilmin harkokin soja Mr.Zhao Xiaozhuo ya ce, "Bayan gyare-gyaren, an kawar da irin hadin gwiwar aikin soja da aka saba yi na dogara ga rundunar sojan kasa, don haka, hadin gwiwar aikin soja da ake gudanarwa yanzu haka na zahiri ne, nau'o'in rundunonin soja suna zama daidai wa daida da juna. Muna kafa shiyyoyin soja, ko wace shiyyar soja kuma tana da alkiblarta ta musamman, abin da ka iya taimakawa ga share fagen daukar matakan soja idan bukatar haka ta taso, haka kuma zai taimaka ga inganta kwarewar soja bisa burin da ake son cimmawa."

A sa'i daya, gyare-gyaren sun kuma gaggauta inganta makaman da sojojin kasar suke amfani da su, inda aka fara aiki da jirgin ruwan soja da jiragen saman yaki ke sauke a kansu da kasar Sin ta kera, tare kuma da sabbin nau'o'in jiragen saman soja, wannan ya inganta kwarewar rundunar sojojin kasar.

Ba za a raba bunkasuwar kasar Sin da zaman lafiyar duniya ba. A cikin 'yan shekarun baya, sojojin kasar Sin na kara taka rawa a fannonin kiyaye zaman lafiya a duniya da ba da kariya ga zirga-zirgar jiragen ruwa a tekunan duniya da samar da agajin jin kai da sauransu. A matsayinta na kasar da ke da kujerar dindindin a kwamitin sulhun MDD, kasar Sin ta kasance a kan gaba wajen tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa sassan duniya. Sa'an nan, daga cikin jiragen ruwa sama da 6000 da rundunar sojan ruwa ta kasar ta ba su kariyar zirga-zirga, sama da rabi jiragen ruwa ne na kasashen waje ko kuma na hukumar tsara shirin abinci ta duniya (WFP). Baya ga haka, a kokarin neman kubutar da fasinjojin jirgin saman nan na Malaysia sanfurin MH370 da kuma yaki da cutar Ebola a Afirka, sojojin kasar Sin sun taka rawa a wadannan fannoni. Haka kuma sojojin kasar Sin suna kokarin dauke nauyin da ke bisa wuyansu na kiyaye zaman lafiya a duniya.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China