in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AfDB zai baiwa Somaliya da Sudan ta kudu dala miliyan 78.6 don magance fari
2017-08-02 11:00:09 cri
Bankin raya ci gaban kasashen Afrika (AfDB) ya kulla yarjejeniyar ba da dala miliyan 78.6 ga gwamnatocin kasashen Somaliya da Sudan ta kudu domin su yi amfani da kudaden wajen shawo kan matsananciyar yunwa da karancin abinci mai gina jiki da kasashen suke fama da su sakamakon fari.

AfDB ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa inda ya ce, ya baiwa Somaliya dala miliyan 34.8 don tallafawa mutane kimanin 804,000 yayin da ya bayar da dala miliyan 43.8 ga Sudan ta kudu domin tallafawa mutane 300,000.

Bankin na Afrika ya kuma cimma matsaya da kungiyar raya ci gaban gabashin Afrika (IGADF) inda bankin ya ce, babu sauran wani shirin ba da tallafin gaggawa na gajeren zango don yaki da yunwa wato (STRERP) a halin yanzu.

AfDB ya sanar da cewa IGADF za ta sanya ido domin duba yadda za'a aiwatar da wannan shirin a kashen biyu.

Karkashin wannan shirin, bankin ya shirya zuba jarin dala biliyan 1.1 domin gudanar da ayyuka a mambobinta da dama wadanda matsalar fari ta dogon lokaci ta shafa.

Hukumomin za su yi aiki tare da gwamnatoci domin tsarawa, da samar da muhimman kayayyakin da ake bukata wanda zai ba su damar kara daukar matakan da suka dace wajen kula da matsalolin annoba da rarraba kayan tallafi ga wadanda suke cikin bukata. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China