in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a tsara sabon tsarin gudanar da harkokin asibitin gwamnatin Sin nan da 2020
2017-07-27 10:27:34 cri

Kwanakin baya ofishin aikin majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wata takarda, inda aka gabatar da ra'ayin ba da jagoranci kan aikin tsara sabon tsarin gudanar da harkokin asibitocin dake karkashin mallakar gwamnatin kasar nan da shekarar 2020.

A yayin taron watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, mataimakin shugaban darektan hukumar kiwon lafiya da shirin iyalai ta kasar Sin, kuma darektan ofishin yin kwaskwarima kan aikin likitanci na majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Hesheng ya bayyana cewa, yana da muhimmanci a kara mai da hankali kan huldar dake tsakanin asibiti da gwamnati, saboda hakan zai taimaka wajen tsara tsarin gudanar da harkokin asibitoci mallakar gwamnati, wanda zai dace da yanayin da ake ciki a halin yanzu, kana idan ana son tafiyar da harkokin asibitin gwamnati yadda ya kamata, to, dole ne a hana a sayar da magungunan sha ga majinyaci fiye da bukatarsa.

Bisa alkaluman da aka gabatar, ya zuwa karshen shekarar 2016, gaba daya adadin asibitocin gwamnatin kasar Sin ya kai dubu 12 da 708, adadin da ya kai kaso 40 bisa dari daga cikin daukacin asibitoci a fadin kasar ta Sin, adadin likitocin asibitocin gwamnatin kuwa ya kai miliyan 5 da dubu 340, adadin gadojin asibitocin ya kai miliyan 4 da dubu 455, adadin da ya kai kaso 80 bisa dari daga cikin daukacin adadinsu a kasar, ko shakka babu asibitocin gwamnatin suna taka muhimmiyar rawa a kasar ta Sin, a saboda haka sun kasance asibitoci mafiya muhimmanci da gwamnatin kasar ke gudanar da aikin kwaskwarima a kai.

Bisa takardar ba da jagoranci kan aikin tsara sabon tsarin gudanar da harkokin asibitocin gwamnatin da ofishin aikin majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar kwanakin baya, an ce, yanzu haka kamata ya yi a nace ga manufar kara mai da hankali kan kiwon lafiyar al'ummar kasar da amfanin samar da moriya ga al'ummar kasa daga asibitocin gwamnati, da kuma kyautata huldar dake tsakanin asibitoci da gwamnati, da haka za a cimma burin tsara sabon tsarin gudanar da harkokin asibitocin gwamnati nan da shekarar 2020.

Mataimakin shugaban darektan hukumar kiwon lafiya da shirin iyalai ta kasar Sin, kuma darektan ofishin yin kwaskwarima kan aikin likitanci na majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Hesheng ya bayyana cewa, a baya ba a gudanar da huldar dake tsakanin asibitoci da gwamnati yadda ya kamata ba, shi ya sa a halin da ake ciki yanzu, dole ne a kara mai da hankali kan aikin, yana mai cewa, "Takardar ba da jagorancin da aka fitar ta tabbatar da hakkin gwamnatin kasar, kan aikin gudanar da harkokin asibitocin dake karkashin ta; Misali ikon kafa asibiti, da ikon raya asibiti, da ikon tsai da kuduri kan muhimman batutuwan dake shafar ayyukan asibiti, da ikon samun riba daga asibitoci da dai sauransu."

Wang Hesheng ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi asibitocin gwamnati su amince da gwamnatin kasar game da ikon ta na sa ido kan aikinsu na yau da kullum, domin kara samar da tsaro ga majinyaci.

Bisa bukatar rahoton aikin gwamnatin kasar Sin na shekarar 2017, an ce kafin karshen watan Satumbar bana, za a fara gudanar da kwaskwarima kan aikin asibitocin karkashin mallakar gwamnati a biranen dake fadin kasar daga dukkanin fannoni, tare kuma da hana a kara farashin magungunan sha yayin da ake sayar da su a asibiti. Wang Hesheng ya ce, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, farashin aikin samar da hidima ga majinyata na asibiti yana da araha sosai, ta yadda kudin shiga daga fannin baya iya biyan bukatun gudanarwar asibitocin, a saboda haka dole ne a tsara sabon tsari, yana mai cewa, "Nan gaba za a gyara farashin aikin samar da hidima ga majinyata dake asibitoci, musamman ma kan farashin tiyata, da ganin likita, da ba da jinya daga likitocin gargajiyar kasar Sin, kana za a gudanar da aikin ne bisa matakai daban daban, ta haka za a kara darajar fasahohin likitanci, tare kuma da kyautata tsarin samun kudin shiga na asibitocin."

Kazalika, abu mafi muhimmanci shi ne a cikin takardar, a karo na farko an gabatar da cewa, za a tsara ka'idojin gudanar da harkokin asibitoci a kasar Sin. Mataimakin shugaban asibitin Xiehe na birnin Beijing Yang Dungan ya bayyana cewa, "Yanzu yawancin asibitocin dake karkashin mallakar gwamnatin kasar Sin, ba su tsara ka'idojin aikinsu ba tukuna, hakan ya sa ake gamuwa da matsala yayin ake raya asibitocin, amma bisa tanajin ka'idojin, za a samu taikamo wajen ciyar da hidimomin asibitocin gaba cikin kwanciyar hankali."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China