in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarwarin zaman lafiya a Syria sun samu ci gaba
2017-07-14 11:00:51 cri

Jiya Alhamis manzon musamman na gwamnatin kasar Sin kan batun Syria, wanda yake halartar shawarwarin zaman lafiya a Syria a Geneva Xie Xiaoyan, ya gana da manzon musamman na babban sakataren MDD kan batun Syria Staffan De Mistura, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan yadda za a daidaita matsalar Syria ta hanyar siyasa, daga bisani kuma Xie Xiaoyan da De Mistura, sun zanta da manema labaran kasar Sin, inda suka bayyana cewa, shawarwarin na wannan karo sun haifar da babban ci gaba.

Wannan ne karo na hudu da Xie Xiaoyan ya halarci shawarwarin shimfida zaman lafiya a kasar ta Syria da aka gudanar a birnin Geneva, tun bayan da ya hau mukaminsa na manzon musamman na gwamnatin kasar Sin kan batun Syria. Yayin ziyararsa a Geneva, Xie Xiaoyan ya yi ganawa da wakilan 'yan adawa na Syria, kana ya yi ganawa da wakilan gwamnatin Syria, haka kuma ya yi ganawa da wakilan kasashen Rasha da Amurka wadanda ke shiga tsakani a batun. Xie Xiaoyan yana ganin cewa, shawarwarin na wannan karo sun haifar da babban ci gaba, yana mai cewa, "Na tattauna da manzon musamman na De Mistura, kuma na gana da wasu wakilan da abun ya shafa. Tabbas na ga ci gaban da aka samu bayan shawarwarin da aka yi a Geneva, baya ga ci gaban shawarwarin, a hannu guda an kuma kara cimma ra'ayi daya kan wannan batu."

Xie Xiaoyan ya ci gaba da cewa, shawarwarin zaman lafiya da ake gudanarwa karkashin jagorancin MDD muhimmin mataki ne da aka dauka, a fannin warware matsalar Syria ta hanyar siyasa. Game da shawarwarin da ake gudanarwa a wannan karo, kasar Sin tana sa ran za a samu ci gaba a fannoni uku. Da farko, ci gaba da gudanar da shawarwarin, wato kada a daina, saboda akwai bambanci dake tsakanin sassan biyu, wato gwamnatin Syria da 'yan adawa, shi ya sa ake da bukatar yin shawarwari domin cimma ra'ayi daya da kuma fahimtar juna; Na biyu, dole ne a nace ga ka'idar warware matsalar ta hanyar siyasa; Na uku kuwa, dole a nace ga ka'idar warware matsalar bisa dogaro da al'ummar kasar ta Syria; Wato al'ummar Syria su daidaita matsalar da kansu, kuma kamata ya yi sauran kasashen duniya su bukaci gwamnatin Syria da 'yan adawar ta su yi hakuri su kai zuciya nesa, su yi shawarwari, a karshe ku kai ga tsai da kuduri kan makomar kasarsu, wanda zai dace da babbar moriyar kasar ta Syria, da ta al'ummar ta baki daya.

Xie Xiaoyan ya ce, "Abu mafi muhimmanci shi ne gudanar da shawarwari, domin neman samun wata dabarar da za ta samu amincewa daga fannoni daban daban, ta haka ne kuma za a warware matsalar da ake fuskanta ta hanyar siyasa yadda ya kamata. Har kullum kasar Sin tana kokari kan wannan aiki, kuma za ta ci gaba da kwazo kamar yadda ta saba."

De Mistura shi ma yana ganin cewa, ya ga alama mai faranta ran kowa yayin da ake gudanar da shawarwarin, ya ce, "An ciyar da shawarwari gaba lami lafiya. Da farko dai, daukacin kungiyoyin 'yan adawa na Syria, da kungiyar wakilan gwamnatin kasar ta Syria sun sauka wuri guda sun kuma tattauna. Ba kuma su daina ba, hakika mun yi shawarwari masu ma'ana."

De Mistura ya yi farin ciki, da ganin muhimman kungiyoyin 'yan adawa na Syria uku; wato babban kwamitin shawarwari, da kungiyar Alkahira, da kungiyar Moscow sun shiga shawarwarin da aka shirya har sassan uku, sun tattauna tsakaninsu kai tsaye, game da batutuwan da suke jawo hankulansu duka. Ban da haka kuma De Mistura ya yi shawarwari da kungiyar wakilan gwamnatin kasar ta Syria, kan tsara mulkin kasar, da gudanar da zaben kasar a nan gaba da dai sauransu. De Mistura ya kuma bayyana cewa, duk da cewa kungiyar gwamnatin kasar Syria, da kungiyar 'yan adawa ba su gudanar da shawarwari tsakaninsu kai tsaye ba tukuna, amma yana sa ran cewa, za su cimma wannan buri a nan gaba.

Kaza lika, De Mistura ya godewa kasar Sin saboda kokarin da take yi, domin ingiza shawarwarin zaman lafiya a Syria, kana ya yaba da muhimiyyar rawar da kasar Sin take takawa a kwamitin sulhun MDD, musamman ma kan batun Syria. Misali gwamnatin kasar Sin ta nada manzon musamman nata kan batun, ita ma tana yin kokarin gabatar da wasu shawarwarin da za su taimaka wajen daidaita batun Syria yadda ya kamata.

Za a kammala shawarwarin shimfida zaman lafiya a Syria karo na 7 a Geneva a yau 14 ga watan nan da muke ciki. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China