in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Huang Danian, masanin kimiyya mai kishin kasa na Sin
2017-07-13 10:34:13 cri

Huang Danian, masanin kimiyyar kasar Sin mai shekaru 58 da haihuwa ya riga mu gidan gaskiya a ranar 8 ga watan Janairun bana, kafin rasuwarsa, ya dukufa kan aikin nazarin fasahohin dake da nasaba da yanayin kasa, har ta kai ya samu babban sakamako wanda ya kai matsayin koli a duniya.

Huang Danian ya taba zuwa kasar Birtaniya domin neman karin sani kan ilmomin kimiyya, bayan da ya kammala karatu a jami'ar koyon ilmin yanayin kasa ta Changchun dake lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar Sin, inda ya samu digirin digirgir. Daga baya kuma ya komo nan kasar Sin, duk da cewa, an gabatar masa albashi mai tsoka a kasar ta Birtaniya.

Dalilarsa Zhou Wenyue ta nuna shakku kan shawarar da ya yanke, tana mai cewa, "A wancan lokaci, na tambaye shi, malam Huang, ina dalilin da ya sa ka komo nan kasar Sin aiki a maimaikon zama ka yi aiki a kasar Birtaniya? sai ya gaya mini cewa, ya je kasar waje domin yin karatu ne, shi ya sa bayan da ya kammala karatu, ya komo domin bautawa kasarsa, wato dai babu wani sauran zabe a gabansa."

A shekarar 2009, Huang Danian ya komo kasar Sin inda ya fara aiki a jami'ar Jilin, kusan ko wace rana yana gudanar da aiki a cikin ofishinsa, kuma ya kan sha aiki a wasu lokuta har zuwa karfe biyu ko uku na safiya.

Sakatariyarsa Wang Yuhan ta gaya mana cewa, idan ba a ga hasken fitila a ofishisa ba, to, tabbas ya tafi wasu wurare na daban domin ziyarar aiki.

Har kullum Huang Danian na aiki ba dare ba rana a duk tsawon shekara, har abokan aikinsa su kan dauke shi wani sarkin aikin kimiyya, dalilinsa Ma Guoqing yana mai cewa, "A baya, na kasa fahimtar kaunarsa ga aikin nazarin kimiyya, mutane da dama suna daukar sa wanda bai san me yake yi ba, tabbas ya fita daban wajen binciken nazarin kimiyya, kusan yana shafe dukkan lokacinsa kan aiki, babu hutu sai dai dan barci na gajeren lokaci. Ya kan gaya mana cewa, aikinmu yana da muhimmanci matuka, saboda muna tsara makomar nazarin kimiyya ta kasarmu bisa manyan tsare-tsare. Don haka, makasudin aikinmu shi ne ciyar da sha'anin kimiyya na kasarmu gaba, da kuma bai kamata mu yi la'akari kan moriyar kanmu kawai, dole ne mu mai da hankali kan makomar kasarmu."

Muhimmin aikin Huang Danian na yau da kullum shi ne yin nazari kan wata nau'in na'urar tantance labaran dake karkashin kasa mai zurfi, ana iya amfani da na'urar a fannoni da dama. Misali fannin tantance albarkatun mai da gas, da kuma ma'adinai dake karkashin kasa, haka kuma ana iya amfani da ita a cikin jirgin ruwa mai aiki a karkashin ruwan teku.

Mataimakiyar sa, kuma babbar malama a jami'ar Jilin Yu Ping ta bayyana cewa, "Aikin malam Huang Danian yana da nasaba da zaman rayuwar al'ummar kasar mu, kana ya shafi tsaron kasa, shi ya sa ana iya cewa, fasahar sa na da muhimmanci matuka, kuma a halin da ake ciki yanzu, kasashe kalilan ne suke mallakar wannan fasaha, kusan ma sirri ce ta kasashe a matsayin koli. Lokacin da malam Huang ya komo nan kasar Sin, ya fara gudanar da aikin nazari kan wannan fasaha, tare da fitattun masu aikin kimiyya sama da dari daya, abu mai faranta ran mutane shi ne sun samu sakamako bayan da suka shafe shekaru biyar suna aikin."

Yayin da malam Huang Danian ya kammala karatu a jami'ar koyon ilimin yanayin kasa dake Changchun, ya rubuta wasu kalmomi cikin wani littafi kamar haka: farfado da kasar Sin, nauyi ne dake bisa wuyanmu. Bisa wannan tunanin, malam Huang ya fi mai da hankali kan aiki sama da komai, maimakon lafiyar jikin sa, shi ya sa ya kan hadu da ciwon ciki har ya suma yayin da yake aiki, amma ba ya so ya je asibiti. kullum yakan ce ba shi da lokaci, yana karancin lokacin aiki, daga karshe an kai shi asibiti, abu mai bakanta rai a nan shi ne sakamakon binciken da aka yi masa a asibiti ya nuna cewa, ya kamu da kansar koda.

Ko da a kan gadon asibiti, malam Huang Danian bai daina aiki ba, har gaf da lokacin da za a yi masa tiyasa, inda ya komo ofishinsa ya ci gaba da aiki yadda ya saba har zuwa tsakar dare.

Bayan tiyata, bai komo aiki ba kamar yadda aka yi fata, ya riga mu gidan gaskiya a ranar 1 watan Janairun bana, yana da shekaru 58 da haihuwa.

Ga wakar da malam Huang Danian ya fi son saurara, "Ina kaunar ki, kasar Sin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China