in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasan tsallake igiya
2017-07-13 08:49:19 cri

Wasan tsallake igiya da yadda ake yinsa a kasar Sin


Wasan tsallake igiya wato wasan da ake kira "skipping rope" ko kuma "jump rope" a Turance, daye ne daga wasanni masu farin jini a duniya. Mutane da yawa na kasashe daban daban na amfani da wannan wasa domin motsa jikinsu.

Dabarar tushe kuma mai sauki ga gudanar da wasan ita ce, a rike karshen igiya da hannu, a yi ta juya igiyar, yayin da ake tsalle, ta yadda igiyar za ta rika wucewa ta karkashin kafafuwan mutum. Ka ga wasan yana da sauki.

Duk da cewa akwai sauran fasahohi masu sarkakiya dangane da wasan, amma kayan da ake bukata wajen gudanar da wasan igiya ce kawai. Kuma babu bukatar samun fili na musamman. Ko a cikin gida ma za a iya gudanar da wasan. Saboda haka a ko ina a duniya, idan ka shiga cikin wuraren da jama'a suke motsa jikinsu, to, akwai yiwuwa za ka gamu da wasu da suke wasan tsallake igiya.

A nan kasar Sin, gwamnati tana kokarin yayata wasan tsallake igiya, a matsayi wata dabarar kare lafiyar jikin al'umma. Saboda haka, kusan a dukkan makarantun kasar, malamai suna koyar da fasahar tsallake igiya, kuma a kan sanya dalibai su shiga gasanni domin gwada fasaharsu a wannan fanni. Bayan mutum ya girma kuma, ba zai rasa damar halartar wasan tsallake igiya ba, domin kamfanoni daban daban su kan shirya gasar tsallake igiya, domin baiwa ma'aikata damar motsa jikinsu. Ga misali, a nan CRI, kungiyoyin ma'aikata su ma su kan shirya gasannin tsallake igiya. Akwai gasa ta mutum daya, inda a kan kirga yawan adadin da mutumin ya tsallake igiyar cikin minti daya, haka kuma akwai gasar da mutane da yawa su kan shiga a lokaci guda, inda aka sanya mutane 2 su yi ta juya igiya, yayin da sauran mutanen suka tsallake igiyar daya bayan daya. Bayan mintuna 3, sai a yi kirgar yawan mutanen da suka yi nasarar tsallake igiyar. Ta wannan misali, za ka iya gano cewa, wasan tsallake igiya tamkar wani wasa ne na kowa a nan kasar Sin.

Dalibai suna gudanar da wasan a makarantu, yayin da baligai kuma ke halartar wasan a wuraren aikinsu. Wannan shi ne yanayin da Sinawa suke ciki ta fuskar rungumar wasan tsallake igiya.

Amfanin wasan ga lafiyar jikin dan Adam

Yadda ake karbar wasan tsallake igiya a dukkan bangarorin kasar Sin da kasar Najeriya ya nuna cewa, ana kallon wasan a matsayin wata hanya mai kyau wajen motsa jiki da kare lafiyar jikin dan Adam. Masu ilimin lafiya sun ce, wasan tsallake igiya, yana da amfani daya da na wasan gudu da kuma sassarfa, wato zai iya taimakawa kyautata yanayin zuciya da huhu na dan Adam. Haka kuma wasu kwararrun 'yan wasa da yawa, suna amfani da wasan tsallake igiya a matsayin dabarar rage kiba da nauyin jikinsu, ganin yadda wasan ya ke daya daga cikin wasannin da suka fi amfani wajen rage kibar mutum cikin sauri.

An ce, idan mutum zai yi wasan tsallake igiya tsawon sa'a daya, to, hakan zai ba shi damar rage kiba, tare da kone makamashin jiki da ya kai "Calory" 700 zuwa fiye da 1000. Wato ke nan, yawan kibar da za ta ragu sakamakon tsallake igiya na tsawon mintuna 10, yana daidai da yawan kibar da za ta ragu, bayan da aka yi gudun tsawon mil daya cikin mintuna 8.

Mu dubi mutanen dake kewayenmu, a kan ga mutanen da suke juyayin cin abinci fiye da kima. Musamman ma mata, wadanda ke son samun suffar jiki mai kyan gani. Idan ta kasa hakuri ta ci askirim, ko kuma sukari, za ta yi nadama sosai. Amma idan za ta iya wasan tsallake igiya, to babu bukatar da-na-sani. Saboda tsallake igiya har tsawon mintuna 15 zuwa 20, zai bada damar rage "Calory" ko kuma yawan kibar da aka samu bayan shan wani nau'in sukari na "Alawa". Ka ga amfanin wasan tsallake igiya a fannin rage kiba ke nan.

Mun san samun kiba da yawa fiye da kima daya ne daga cikin manyan dalilan da suke haddasa mutuwa. Don haka ta hanyar shiga wasan tsallake igiya, za a iya kare lafiyar jikin mutum, har ma hakan ya ba da damar karin tsawon rai.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China