170726-Rawar-da-sojojin-yantar-da-alumma-na-Sin-suka-taka-a-kasashen-duniya.m4a
|
Sojojin 'yantar da al'umma ta kasar Sin, ita ce runduna mafi girma a duniya. Koda yake a watan Satumban shekarar 2015, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi alkawarin rage dakaru 30,000 daga cikin sojojin.
Ita dai rundunar sojojin 'yantar da al'umma ta kasar Sin tana karkashin hukumar kula da harkokin soja ta kasar. Kuma ayyukan rundunar sun hada da kula da tsaron lafiyar fararen hula baya da tabbatar da tsaron kan iyakokin kasar.
Duk da wannan babban nauyin dake kan sojojin, suna kuma ba da gudummawa a fannonin bala'u daga indallahi, ambaliyar ruwa, girgizar kasa da sauran hidimomi da al'umma ke bukata. Suna kuma taka rawa a ayyukan kiyaye zaman lafiya karkashin laimar MDD a sassa daban-daban na duniya, kamar kasashen Lebanon,Jamhuriyar demokiradiyar Congo, Sudan. Sauran sun hada da Ivory Coast da Haiti, Mali, Sudan ta kudu, Liberiya, Saliyo da sauransu.
Bayanai na nuna cewa, sojojin na kasar Sin sun kuma samu lambobin yabo a dukkan wuraren da aka turo su don gudanar da irin wadannan ayyuka na tabbatar da zaman lafiya.(Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)