in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yabawa kokarin Sin wajen kiyaye kayayyakin tarihi
2017-07-05 11:11:28 cri

A yanzu haka ana gudanar da taron kwamitin kula da kayan tarihi na kungiyar UNESCO karo na 41 a birnin Krakow na kasar Poland, kuma wannan shi ne karo na farko da kasar ta Poland ta shirya irin wannan taro.

Za a shafe kwanaki 11 ana gudanar da taron kwamitin kula da kayan tarihi na kungiyar UNESCO karo na 41 a birnin Krakow na kasar Poland, inda za a duba ayyuka guda 34 dake shafar aikin kiyaye kayayyakin tarihi, a cikin wadannan ayyukan, akwai guda biyu da gwamnatin kasar Sin ta gabatar wato ni'imtaccen wurin Kekexili na lardin Qianghai, da tsibirin Gulangyu dake birnin Xiamen na lardin Fujian wadanda ake fatan za su shiga jerin sunayan kayayyakin tarihin hallitu da na al'ada da za a tantance domin samun amincewar kwararrun da abin ya shafa. Idan aka cimma burin, adadin kayayyakin tarihin kasar Sin da suka samu amincewar kwamitin kula da kayan tarihi na kungiyar UNESCO zai kai 52, wanda baya ya kai 50 kawai.

A ranar 3 ga wata ne, wakilai masu shirya babban taron suka kira wani taron ganawa da manema labarai a cibiyar taron dake birnin Krakow na kasar ta Poland, inda suka amsa tambayoyin manema labarai.

A zantawarsa da manema labarai, mataimakin firayin ministan kasar Poland, kana ministan kula da al'adu da kayayyakin tarihi na kasar Piotr Glinski ya bayyana cewa, kasarsa ta Poland ta dade da kulla yarjejeniyar kiyaye kayayyakin tarihin duniya, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kwararrun kasar suna kokari matuka a wurare daban daban a fadin duniya domin taimakawa mabukata, ana iya cewa, kasar ta Poland ta samu wasu sakamako a wannan fannin, shi ya sa ta samu damar shirya irin wannan babban taron, wanda ya samu wakilai mahalarta sama da 2000 da suka zo daga kasashe kusan 140. Ban da haka kuma, firayin minista Glinski ya bayyana cewa, kamata ya yi kasarsa da kasar Sin su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin kiyaye kayayyakin tarihi, yana mai cewa, "Muna fatan yin hadin gwiwa tare da kasar Sin ba tare da wata rufa-rufa ba, ko shakka babu sassan biyu wato Sin da Poland za su samu babban sakamako a wannan fannin, kana kamar yadda na fada, kwararru a fannin kiyaye kayayyakin tarihi na Poland sun kware matuka a wannan aikin, musamman ma wajen sake gina birane, misali sake gina biranen da aka rushe sakamakon yake-yake."

Shehun malami Jacek Purchla wanda shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin kungiyar UNESCO na kasar Poland, kana shugaban babban taron kwamitin kula da kayan tarihi na kungiyar UNESCO karo na 41 ya bayyana cewa, kasar Poland ta shafe kusan shekaru 40 ta na jiran samun damar shirya irin wannan babban taro, Hakika suna jin dadin aikin, yana mai cewa, "za mu nunawa al'ummomin kasashen duniya sakamakon da muka samu a fannin kiyaye kayayyakin tarihi, a sa'i daya kuma za mu tattauna tare da takwarorinmu a yayin taron, tare kuma da yin musanyar fasahohin da muka samu kamar yadda muke so. Mun san kasar Sin ita ma ta kware a aikin kiyaye kayayyakin tarihi, a baya na taba kai ziyara birnin Xi'an na lardin Shaanci na kasar Sin inda na kalli mutum mutumin da aka sassaka da tukwane wanda ya shahara a fadin duniya, ina ganin cewa, irin wannan kayan tarihi alama ce ta tarihin kasar Sin, ba zan manta da su ba har abada, haka kuma ana iya cewa, mutum mutumin da aka sassaka da tabo na kasar Sin sun alamanta cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako a fannin kiyaye kayayyakin tarihi."

A shekarar 1985 ne .kasar Sin ta daddale yarjejeniyar kiyaye kayayyakin tarihin duniya, har kullum tana dukufa kan aikin kiyaye kayayyakin tarihi, babbar jami'ar kungiyar UNESCO Irina Bokova ta yabawa kasar Sin saboda kokarin da take a wannan fannin, ta ce, kasar Sin tana da dogon tarihi, kana tana kokarin kiyaye kayayyakin tarihi. Tana mai cewa, "A ganina, bisa bunkasuwar kasar Sin, kasar Sin ita ma tana fuskantar kalubale mai tsanani a fannin kiyaye kayayyakin tarihi, misali kazantar muhalli da sauransu, a saboda haka, domin biyan bukatun kasar ta Sin, ina ganin cewa, ya zama wajibi a bullo da wasu tsare-tsare domin kara kyautata aikin kiyaye kayayyakin tarihi, dalilin da ya sa haka shi ne kayayyakin tarihi dukiyoyi ne na daukacin bil Adama."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China