in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ilmin likitanci da maganin gargajiya na Sin ya samu yaduwa a kasashe 183
2017-06-29 13:55:10 cri

Daga ranar 6 zuwa 7 ga wata mai zuwa, za a kira taron ministocin kiwon lafiya na kasashe mambobin BRICS, kuma babban taron ilmin likitanci da maganin gargajiya na kasashen a birnin Tianjin da ke nan kasar Sin. Mataimakin shugaban sashen kula da aikin hadin gwiwa da kasashen waje na hukumar kula da ilmin likitanci da maganin gargajiya ta kasar Sin Zhu Haidong ya bayyana cewa, kasashe mambobin BRICS manyan kasashe ne a fannin ilmin likitanci da maganin gargajiya, ana kuma fatan za a sa kaimi ga bunkasuwar ilmin ta wannan taron, a kokarin amfanawa jama'ar kasashe mambobin BRICS da ma na duniya baki daya. Bisa labarin da aka samu, an ce, ya zuwa yanzu ilmin likitanci da maganin gargajiya na kasar Sin ya samu yaduwa a kasashe 183.

Yanzu bari mu hada bakin abokiyar aikinmu Kande, mu ji cikakken rahoto.

A yayin wani kwas din horar da ilmin allurar gargajiyar kasar Sin da wata kungiyar likitanci ta kasar Jamus ta shirya a watan Mayu na bana, likitoci matasa fiye da goma na koyon ilmin jijiyoyi na gargajiyar kasar Sin. Furofesa Schwanitz da ke ba da ilmi a gabansu na da shekaru 72 da haihuwa, tana kuma dukufa kan aikin yin allurar gargajiyar kasar Sin da aikin koyarwa a Jamus cikin tsawon fiye da shekaru 40. Furofesa Schwanitz ta bayyana cewa, "Ilmin likitancin gargajiyar kasar Sin ya sha bamban sosai da na yammacin duniya, wanda ke ba mu wahala sosai wajen gane ainihin yadda yake. Mutanen da suka zo karatu yau ba su da yawa, kullum wannan kwas na horaswa namu kan jawo mutane kusan 30, inda mu kan tattauna, da koyar da yadda za a yi wa mutane allurar gargajiyar kasar Sin."

Masu sauraro, ta wannan tsokaci muna iya gano cewa, yanzu haka ilmin likitanci da magani na gargajiyar kasar Sin yana ta samun babban tasiri a kasashen duniya. Mataimakin shugaban sashen kula da aikin hadin gwiwa da kasashen waje na hukumar kula da magungunan gargajiya ta kasar Sin Zhu Haidong ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta riga ta daddale yarjeniyoyi 86 tare da gwamnatocin kasashen waje, da kungiyoyin duniya kan ilmin likitanci da magani na gargajiyar kasar Sin. Yanzu kuma ilmin likitanci da magani na gargajiyar Sin ya riga ya zama wani muhimmin kashi na kara mu'amalar al'adu a tsakanin Sin da kasashe daban daban. Kana ya zama wani bangare mai muhimmnaci dake kara kawo alheri ga bil Adam, gami da raya makomar bil Adam baki daya. Zhu Hai Dong ya kara da cewa, "A fannin aikin koyar da ilmin likitanci da magani na gargajiyar kasar Sin, akwai kasashe fiye da 30 da suka kafa makarantu, da kwalejoji daruruwa na koyar da ilmin maganin gargajiyar Sin, bisa aniyar horar da kwararrun su a wannan fanni. Bugu da kari, a ko wace shekara, akwai dalibai fiye da 13000 da ke da damar zuwa kasar Sin don kara ilminsu a wannan fanni, yayin da mutane fiye da dubu 200 ke zuwa kasar Sin don samun jinya bisa hanyar shan maganin gargajiya. Haka kuma, kasar Sin ta tura tawagar ba da jinya zuwa kasashe fiye da 70, a cikin su, yawan likitoci masu rike da ilmin likitancin gargajiya na kaiwa kaso 10 cikin dari. Bugu da kari, ilmin likitanci da magani na gargajiyar kasar Sin yana amfani a fannin shawo kan manyan cututtuka. Alal misali, dabarar shawo kan cutar malariya ta hanyar amfani da artemisinin tana samun yaduwa sosai a kasashen da ke kudu maso gabashin Asiya, da na nahiyar Afirka, wadda ta rage yawan masu kamuwa da cutar, da kuma kubuta da dimbinsu daga hadarin rasa rayuka."

Haka zakila Mr. Zhu Haidong ya ce, sakamakon kara karbuwa da kasa da kasa ke nuna wa ilmin likitanci da magani na gargajiyar kasar Sin, yanzu ilmin na gaggauta isa ketare. Yana mai cewa, "Ya zuwa yanzu, ilmin likitanci da magani na gargajiyar kasar Sin ya riga ya samu yaduwa a kasashe 183. Bisa kididdigar da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fitar kan hakan, an ce akwai kasashe mambobinta 103, da suka amince da hanyar yin allurar gargajiyar kasar Sin, a ciki, 29 sun kafa dokar amincewa da ilmin likitancin gargajiya, 18 kuma sun shigar da hanyar yin allurar gargajiyar kasar Sin cikin tsarin inshora na kiwon lafiyar su. Har wa yau an riga an yi wa maganin gargajiyar Sin rajista a kasashen Rasha, da Cuba, da Vietnam, da Singapore, da Hadaddiyar Daular Larabawa da dai sauransu. Yawan kudin da aka samu daga safarar maganin gargajiyar Sin zuwa ketare ya kai dala kusan biliyan 3.5 a shekarar 2016."

Ban da kasar Sin, kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Afirka ta Kudu, wato mambobin kungiyar BRICS, su ma manyan kasashe ne a fannin ilmin likitanci da maganin gargajiya. Domin sa kaimi ga ci gaban ilmin, ta yadda zai kara amfanar jama'a, daga ranar 6 zuwa ranar 7 ga wata mai zuwa, za a kira taron ministocin kiwon lafiya na kasashe mambobin BRICS, kuma babban taron maganin gargajiya na kasashen a birnin Tianjin.

Game da hakan, Zhu Haidong yana ganin cewa, taron zai ba da taimako wajen kyautata amincewar da ake nuna wa ilmin likitancin gargajiya, da kuma karfin takarar sa a duniya. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China