in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin karamar sallah a kasar Sin
2017-06-28 13:33:25 cri

A ranar Litinin 26 ga watan Yunin shekarar 2017 ne musulmi a sassa daban-daban na duniya ciki har da nan kasar Sin suka yi bikin karamar sallah na wannan shekara, bayan shafe tsawon wata guda ana Azumin watan Ramadan wato daya daga cikin shika-shikan musuluncin nan guda biyar. Koda yake wasu kasashe kamar Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Malaysia da Indonesia da Saudiya da sauransu sun yi tasu sallar a ranar 25 ga wata.

Kamar sauran kasashen musulmi na duniya haka ma a nan kasar Sin, musulmai suka yi tururuwa zuwa masallatai da ke wurare daban-daban a wannan rana don gudanar da sallah mai raka'a biyu suna sanye da sabbin tufafi cikin farin ciki da annashuwa.

Sai dai ba kamar yadda aka saba yin hawan dabba ko dawakai a lokutan sallah a kasashenmu na Afirka inda ake kade-kade da bushe-bushe a irin wannan rana, a nan lamarin ya sha bambam kamar yadda masu iya magana ke cewa, "Allah daya gari bambam". Sai dai su ma musulmai da ke nan kasar Sin kan yi irin nasu shagulgulan da gaishe-gaishe da nau'o'in abinci da ake dafawa don murnar wannan rana.

Abu mai muhimmanci a nan Sin shi ne yadda ake samar da matakan tsaro a ranakun sallar Azumi da Lahiya da ma sauran lokutan da musulmai ke gudanar da salloli a masallatai a duk fadin kasar ta Sin.

Amma duk da irin bambancin da ke akwai, musulmai 'yan kasashen waje da ke nan Sin sun yi karamar sallah cikin farin ciki sai dai abin da ba za a rasa ba na kadaici, kuma masu salon magana na cewa, sallah bikin daya rana, ta tafi ta bar wawa da bashi. Muna fatan Allah ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a duniya baki.

Sai kuma wata shekara ga mai sauran numfashi, Allah ya maimaita mana da alheri, Amin. (Ahmed, Fa'iza, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China