170621-Muhimmancin-dandalin-CATTF-ga-hadin-gwiwar-Sin-da-Afirka.m4a
|
Sai dai duk da wannan rashin fahimta da irin wadannan kasashen ke yi wa dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, shugabannin kasar Sin sun jaddada cewa, babban tushen dake tsakanin Sin da Afirka ba zai canja ba.
Alkaluma sun nuna irin tallafi da moriyar da kasashen Afirka suka samu daga wannan dangantaka a bangarori daban-daban kamar su al'adu, ilmi, makamashi, sufuri, tattalin arziki, kiwon lafiya, fasahohin aikin gona, yawon bude ido da sauransu.
Saboda muhimmancin wannan dangantaka tsakanin bangarorin biyu, har ta kai ga kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, abin dake kara nuna karfafa wannan dangantaka mai tarin alheri ga sassan biyu. Wannan shi ya haifar da kafuwar dandanlin masu ruwa da tsaki a fannonin cinikayya, siyasa, ilimi, tsaro da sauransu wato CATTF a takaice a shekarar 2011.
Tun daga wancan lokaci har zuwa yanzu, masana daga bangarorin ke ganawa a kowace shekara a mabanbantan wurare domin tattauna sabbin hanyoyi da matakan karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Sauran muhimman fanonnin sun hada da aiwatar da ajandar raya nahiyar Afirka nan da shekara ta 2063, dangantakar Afirka da sauran kasashen duniya, da kuma abubuwan da bangarorin biyu za su koya daga juna.
Masu fashin baki na cewa, muddin ana bukatar cin gajiyar wannan dangantaka yadda ya kamata, wajibi ne bangarorin biyu su mutunta alkawuran da suka cimma, mutunta juna, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu a bangarori gwamnatoci da al'ummomin sassan biyu. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)