in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fidda rahoto game da sauke nauyin dake wuyen kamfanin Sin kan aikin ginawa layin dogo na SGR
2017-06-16 11:08:09 cri

A ranar 29 ga watan Mayu, watau kafin sabon layin dogo tsakanin biranen Mombasa da Nairobi ta kasar Kenya wato SGR a takaice ya soma aiki, kamfanin gina kayayyakin zirga-zirga na kasar Sin watau CCCC wanda ya gudanar da aikin gina layin dogon, ya kira taron karawa juna sani kan rahotanni guda biyu masu take "rahoto game da sauke nauyin dake wuyan kamfanin CCCC na shekarar 2016", da kuma "rahoto game da sauke nauyin dake wuyen kamfanin CCCC kan aikin ginawa layin dogo na SGR na shekarar 2016" a birnin Nairobi na kasar Kenya. Kuma wannan shi ne karo na farko da kamfanin kasar Sin ya fidda rahoton sauke nauyi a kasashen ketare.

Bayan wannan taro kuma, masana na bangaren kasar Sin da na kasar Kenya sun yi tattaunawa kan damammaki, da kalubaloli dake gabanmu, a yayin da za a habaka hadin gwiwa bisa shawarar "hanya daya da ziri daya". Dangane da wannan harka, ga karin bayani da Maryam Yang ta hada mana:

Rahoton na sauke nauyi da kamfanin CCCC ya fitar a wannan karo, ya yi bayani kan muhimmiyar rawa da kamfanin ya taka a fannonin gina layin dogo mai inganci, da ba da kyakkyawan horo ga ma'aikatan kamfanin, da hadin gwiwa da abokan kamfanoni yadda ya kamata, da kuma neman dauwamammen ci gaba na muhallin duniya da dai sauransu, inda ya kuma yi cikakken bayani kan manufofin gudanawar ayyukan kamfanin, tare da fitar da wasu ainihin kididdigar da ya yi, domin yin musaya da bangarorin dake da nasaba da shi.

Haka kuma, layin dogo na SGR wanda reshen kamfanin CCCC, watau kamfanin gina layin dogo da gadoji na kasar Sin na CRBC ya gina a kasar Kenya, ya kasance babban burin kasar Kenya cikin jadawalinta na neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030, wanda ya kuma kasance babban layin dogo cikin layukan dogo dake yankin Afirka ta gabas, inda zai ba da babbar gudummawa ga bunkasuwar ma'amala a tsakanin kasashen dake yankin da kuma ci gaba na tattalin arzikin yankin baki daya.

A sa'i daya kuma, cikin rahoto game da sauke nauyin dake wuyan kamfanin CCCC kan aikin gina layin dogo na SGR na shekarar 2016 da kamfanin ya samar mai shafuna 90, an yi bayani na rubutu, da na hotuna kan ayyukan ginawar layin dogon SGR, da kuma tasirin da mai iyuwa layin dogon zai samar wa bangarorin da abin ya shafa. Haka kuma, an yi bayani kan yadda aka gudanar da ayyukan da abin ya shafa bisa manufar girmama hakkin dan Adam, da dokokin yankin, da kuma ka'idoji na kasa da kasa, ta yadda aikin zai ba da gudummawa yadda ya kamata wajen raya tattalin arziki, da kiyaye muhalli, da kuma tabbatar da zaman lafiya da zaman karko a yankin.

Bisa kididdigar da aka yi ,an ce, a yayin da ake gudanar da aikin gina layin dogon mai tsaron kilomita 472, gaba daya an samar da guraban aikin yi kimanin dubu 46 ga 'yan kasar Kenya, kana an horar da ma'aikatan wurin dubu 18.

A yayin taron da aka yi, jakadan kasar Sin dake kasar Kenya Liu Xianfa ya bayyana cewa, kamfanonin kasar Sin su sauke nauyinsu yadda ya kamata, ta hanyar da ta dace a cimma burin neman ci gaba tare, haka kuma, zai ba da taimako ga kamfanonin kasar Sin waje samun bunkasuwa yadda ya kamata kuma cikin sauri. A 'yan shekarun nan, kamfanonin kasar Sin dake kasar Kenya, da mutanen kasar Sin dake kasar, su kan sauke nauyin dake wuyansu cikin himma da kwazo, lamarin da ya sa, aka samun sakamakon da dama bisa kokarin da suka yi, kamar batun samar da karin guraben aikin yi, da kyautata fasahohin da aka yi amfani da su, da kuma inganta bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al'umma a kasar da dai sauransu.

Mataimakin shugaban kamfanin gina kayayyakin zirga-zirga na kasar Sin watau CCCC Chen Yun ya bayyana cewa, cikin dogon lokaci, kamfaninsa yana mai da hankali matuka kan neman bunkasuwa, yayin da yake ba da gudummawa ga zaman takewar al'umma yadda ya kamata, yana kuma sa ran karfafa mu'amalar dake tsakaninsa da bangarorin dake da nasaba da shi, ta yadda za a karfafa fahimtar juna a tsakaninsu, tare da kuma cimma moriyar juna.

Haka kuma, ya ce a nan gaba, kamfanin CCCC zai bi shawarar "ziri daya da hanya daya"da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar, domin ba da Karin gudummawa wajen zurfafa zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasar Kenya, da kuma samar da Karin tallafi ga bangarorin da abin ya shafa.

Daga bisani kuma, shugaban kamfanin gina layin dogo da gadoji na kasar Sin wato CRBC Lu Shan ya yi bayani kan yadda kamfaninsa ya sauke nauyin dake wuyansa, a yayin da ake gudanar da ayyukan gina layin dogon SGR bisa fannoni guda biyar da suka hada da, tabbatar da ingancin layin dogon, da kiyaye muhalli, da tallafawa al'umma, da cimma moriyar juna da kuma taimaka wa jama'ar yankin bisa bukatunsu.

Haka zalika, ya ce, kamfanin CRBC zai ci gaba da yin hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa a kasar Kenya domin neman bunkasuwar kansa, a yayin da sauke nauyin dake wuyansa yadda ya kamata, da kuma ba da gudummawa kan ci gaban zaman takewar al'ummar kasar Kenya.

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake hukumar kiyaye muhalli ta MDD Liu Ning, ya ba da jawabi a yayin taron, yana mai cewa, baya ga dukufa da kasar Sin ke yi wajen neman dauwamammen ci gabanta ta hanyar kiyaye muhalli, a sa'i daya kuma, tana mai da hankali kan fuskantar da kalubalolin muhalli, a yayin dake zuba jari a kasashen ketare, domin inganta ci gaban duniya ta hanyar kiyaye muhalli. Nauyin kiyaye muhalli shi ne muhimmin nauyin dake wuyan kamfanonin kasa da kasa, kuma ita ne, babbar ka'idar tabbatar da gudanarwar shawarar "ziri daya da hanya daya" yadda ya kamata. A yayin da kamfanin CCCC da kamfanin CRBC suka gudanar da aikin ginin layin dogon SGR a kasar Kenya, sun mai da hankali kwarai kan kiyaye muhalli, da kuma neman dauwamammen ci gaba, lamarin da ya sa, gina layin dogon ta kasance abin koyi ga kasar Sin da kasashen Afirka wadanda suke son neman dauwamammen ci gaba.

Mataimakin ministan dake kula da harkokin zirga-zirga, ababen more rayuwa, samar da gidaje da kuma bunkasuwar birane na kasar Kenya Paul Malinga Mwangi ya bayyana cewa, kamfanoni sama da guda 934 wadanda suke samar da siminti, da harkokin katako da kuma na'urorin da abin ya shafa sun nuna cewa, gina layin dogon SGR ta kawo musu babbar moriya, kuma akwai kamfanoni kimanin 300 dake halartar aikin gina layin dogon, sa'an nan, aka kuma ba da horaswa ga al'ummomin kasar masu yawa, lamarin da ya nuna babbar gudummawa da kamfanin CCCC ya bayar a yankin, wajen inganta bunkasuwar tattalin arziki.

Haka kuma, mataimakin ministan harkokin ba da ilmi na kasar Kenya Chad Belio Kipsang ya ce, a yayin da kamfanin CCCC ke gudanar da aikin gina layin dogon a kasar Kenya, ya mai da hankali sosai kan bukatun al'ummar yankin, lamarin da ya dace da burin ba da ilmi na kasashen duniya, sakamakon horaswa da kamfanin ya bai wa ma'aikatan wurin, da fasahohi da kwarewarsu sun samu kyautatuwa kwarai da gaske, bugu da kari, kamfanin ya kuma ba da dama ga daliban wurin, da su kara ilmin game da wannan fanni, ta yadda za su iya samun guraben aikin yi da sauki a nan gaba.

A yayin dake tsokaci kan binciken da aka yi kan aikin gina layin dogon SGR, shugaban hukumar kiyaye muhalli ta kasar Kenya Jeffrey Wahungu ya bayyana cewa, aikin gina layin dogon SGR, ya taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye muhallin yankin, wanda zai iya kasancewa abin koyi ga kasar Kenya, da ma kasashen dake yankin Afirka ta gabas baki daya.

Bugu da kari, magajin garin Massai Limisu Ole Sepiye ya ba da jawabin cewa, layin dogon da aka gina bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Kenya, zai ba da gudummawa matuka wajen ba da ilmi da fasahohi ga mazaunan wurin, yayin da ake karfafa mu'amalar kasashen biyu cikin himma da kwazo.

Haka zalika, bayan taron fitar da rahotannin guda biyu, wasu masana daga manyan jami'o'in kasar Sin da na kasar Kenya, sun yi wani taron musamman don tattaunawa kan damammaki, da kalubaloli dake gaban kasar Sin da kasar Kenya, bisa yadda za su gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu a nan gaba bisa shawarar "ziri daya da hanya daya".

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China