Mene ne yara 'yan kabilar Tibet suke koya a yankin kiwon dabbobi na Guoluo dake lardin Qinghai na kasar Sin? Ana amfani da harshen Tibet a makarantar firamaren garin Dawu dake yankin Maqin, baya ga wasu darussa da suka shafi kabilar Tibet.
Direktan kula da harkokin bada ilmi na makarantar Cai Rangduojie ya bayyanawa 'yan jarida cewa, akwai darasin koyon harshen kabilar Tibet a kowace rana, da darussan koyon harshen kabilar Han, ilmin lissafi, Turanci, rubutu, fasahohin sadarwa, kide-kide da wake-wake, zane-zane, kimiyya, ilmin halittu da sauransu. Ya kuma bayyana cewa, suna da darasin koyar da fasahar rawar Guozhuang. Hakazalika kuma, akwai darasin kan fannoni da yara suke sha'awa, ciki har da wasan kwallon kwando, kwallon kafa, kwallon badminton, kerawa da sauransu. Kuma suna da darasin adabi da dokoki guda daya a kowane mako. (Zainab)