170616-Ana-kokarin-raya-harkokin-yawon-shakatawa-don-rage-talauci-a-garin-Longsheng-na-jihar-Guangxi-Murtala.m4a
|
A arewacin jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta kasar Sin, akwai wani gari mai suna Longsheng, wanda ke kunshe da kabilu kala-kala, ciki har da kabilar Han, da Yao, da Zhuang, da Dong, da Miao, da sauransu. A shekarun baya, babu ruwa da wutar lantarki a wannan wuri, har ma babu hanyoyin mota, abun da ya sa garin Longsheng ya yi fama da kangin talauci a tsawon lokaci. A cikin shirinmu na wannan mako, za mu gabatar muku da wani bayani dangane da yadda ake kawar talauci a wurin ta hanyar raya sana'ar yawon bude ido.(Murtala Zhang)