170614-Ranar-muhalli-ta-duniya-ta-shekarar-2017.m4a
|
An fara bikin ranar ce a shekarar 1974 domin kada fadakar da duniya game da matsalolin da suka shafi muhalli kamar gurbatar teku da yawan karuwa al'umma da dumamar yanayin duniya. Sauran matsalolin sun hada da fatauncin dabbobin daji da tsirran dake kokarin bacewa a doron kasa da sauransu.
Babban taron MDD ne ya tsara wannan rana a shekarar 1972 yayin zaman babban zauren MDD game da muhallin dan-Adam karo na farko, inda aka tattauna yadda za a hada harkokin da suka shafi bil-Adama da na muhalli a waje guda.
Daga bisa ni kuma a shekara 1974 kamar yadda muka ambata a baya sai aka gudanar da bikin farko na ranar bisa taken "Duniya daya tilo" kuma tun daga wancan lokaci har zuwa wannan lokaci, ake gudanar da wannan biki a wannan rana bisa teka daban-daban duk da nufin kawar da tarin matsaloli dake addabar muhallinmu a wannan lokaci.
Daya daga cikin matakan da kasashen duniya suka dauka na magance wannan matsala, ita ce cimma yarjejeniyar birnin Paris game da matsalar sauyin yanayin duniya da sauran yarjejeniyoyi da matakai tsakani kananan da manyan kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa.
Sai dai masu fashin baki na cewa,akwai bukatar kasashe su kawar da batu na siyasa a yayin da ake kokarin magance wannan matsala baki daya. Kana a rika sarrafa kudade da aka ware don tunkurar wadannan matsaloli da suka addabi muhallin da muke zama. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)