in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda musulmi ke azumin watan Ramadan a kasar Sin
2017-06-08 08:52:33 cri

A ranar Asabar 27 ga watan Mayun shekarar 2017 ne musulmai a sassa daban-daban na duniya suka fara Azumin watan Ramadan, daya daga cikin shika-shikan musuluncin nan guda biyar, wato Tauhidi, Sallah, Azumi, Rakkah da kuma zuwa aikin Hajji idan da hali.

A tsawon watan na Ramadan mai tsarki, an hana musulmai ci ko sha da yin jima'i tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana.

Bayanai na nuna cewa, an fara Azumin na bana ne a kasashe da dama na duniya kamar Najeriya, Nijar, Saudiyya, Malaysia, Indonesia, ciki har da kasar Sin mai yawan musulmai kimanin miliyan 20. Kananan kabilun kasar Sin da suka hada da Hui, Uygur, Kazakh, Uzbek, Tajik da Kyrgyz galibinsu musulmai ne suke gudanar da Azumin.

Ana kuma Azumin a kasar Sin a yankuna masu 'yancin cin gashin kansu da larduna da birane ciki har da Gansu da Ningxia da kuma birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Kamar yadda aka saba bisa al'ada ana sa ran kammala Azumin ne a nan kasar Sin a ranar 26 ga watan Yunin wannan shekara ta 2017 da muke ciki. A cewar masana duk da banbancin lokaci, musulmai na jin dadin yin azumi a kasar Sin, ganin yadda ake tanadar da abincin bude baki da na sahur kyauta a kusan dukkan masallatai tun daga fara Azumin har zuwa karshensa da kuma ranar Sallah. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China