170526-Malamai-da-daliban-kwaleji-na-taimakawa-garin-Daming-na-lardin-Hebei-na-kasar-Sin-wajen-kawar-da-talauci-Murtala.m4a
|
Daming, wani gari ne dake birnin Handan na lardin Hebei dake arewacin kasar Sin. Garin Daming ya taba taka muhimmiyar rawa a tarihin kasar Sin, amma yana fama da kangin talauci a halin yanzu. Baya ga gwamnati da hukumomi dake kokarin samar da tallafi wajen yakar talauci, akwai wasu jami'o'i da kwalejoji gami da dalibai wadanda ke bada gudummawarsu a wannan fanni. Za ku iya samun karin bayani cikin shirinmu na wannan mako.(Murtala Zhang)