A jawabinsa, Yang Jiechi ya yi nuni da cewa, kamata ya yi Sin da Japan su yi tunanin koyon darussan da suka faru a baya tare da hange makoma ta gaba, da rike dama da fadada hadin gwiwarsu da warware matsalolinsu, da raya dangantakarsu yadda ya kamata bisa tushen takardun siyasa 4 na kasashen biyu da ka'idoji hudu da suka cimma daidaito a kai.
Yang Jiechi ya jaddada cewa, ya kamata Sin da Japan su daidaita batun tarihi da batun yankin Taiwan da sauran batutuwan dake shafar tushen siyasa na dangankatar dake tsakanin kasashen biyu, da tabbatar da tushen siyasarsu.
A nasa bangare, Fumio Kisida ya bayyana cewa, Japan tana fatan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin. Japan tana son kara yin mu'amala da juna da yin imani da juna a fannin siyasa, da zurfafa hadin gwiwarsu da sada zumunta a tsakanin jama'ar kasashen biyu.
Daga bisani bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan batun nukiliya na zirin Koriya. (Zainab)