Wang Yi ya ce, game da batun zirin Koriya, kasar Sin ta tsaya kan daidaita matsalar ta hanyar tattaunawa bisa kudurin kwamitin sulhun MDD.
Ministan ya kuma jaddada cewa, matakan soji ba za su taimaka wajen daidaita matsalar ba, sai dai ma su kara haifar da matsaloli.
Mr.Wang Yi ya kara da cewa, batun nukiliyar zirin Koriya, ya samo asalin ne daga matsalar tsaro, don haka, ya kamata a daidaita batutuwan da ke haifar da matsala ga sassa daban daban.
Har wa yau, ya ce rashin amincewa da juna shi ne abin da ke hana ruwa gudu wajen daidaita batun nukiliyar zirin Koriya, don haka, kamata ya yi sassa daban daban su kara daukar matakan da za su taimaka ga kulla aminci da juna.
Ministan ya jaddada cewa, Sin da Rasha za su taka kyakkyawar rawa wajen sassauta halin da ake ciki a zirin Koriya da kuma wanzar da zaman lafiya a shiyyar. (Lubabatu)