A watan da ya wuce, an sha samun yawaitar tashe-tashen hankula tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a sassan CAR. Halin da ake ciki a yanzu babban tashin hankali ne sakamakon rahoton da aka samu game da zarge-zargen cin zarafi da kaddamar da hare-hare kan fararen hula da jami'an aikin wanzar da zaman lafiya, da masu aikin jin kai a kasar. Wadannan jerin laifuka sun kunshi irin laifukan dake karkashin hurumin ICC, don haka dole ne a dakatar da su, in ji Bensouda.
Ta ce, ofishinta yana bibiyar wadannan al'amurra tare da yin nazari game da irin matakan da ya dace a dauka a nan gaba. Ta ce a shirye suke su tallafawa hukumomin CAR wadanda suke da babban nauyi a wuyansu, na farko shi ne dole su gudanar da bincike kuma su garfanar da wadanda ake zargi da aikata laifukan a gaban shari'a. (Ahmad Fagam)