in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon ministan harkokin wajen Habasha ya zama sabon darekta janar na WHO
2017-05-24 11:11:26 cri

Tun a karshen watan Afrilun bara ne aka fara shiryen-shiryen zaben sabon babban darektan hukumar kiwon lafiya ta duniya kana a watan Janairun bana, aka tabbatar da mutane uku daken takarar wannan mukami, wadanda suka hada da, tsohon ministan harkokin wajen kasar Habasha Tedros Adhanom, da tsohuwar ministar tarayya mai kula da harkokin kiwon lafiya, ilimi da kimiyya da fasaha ta kasar Pakistan Sania Nishtar, da kuma mashawarci na musamman ga sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya David Nabarro daga kasar Birtaniya.

A yayin babban taron kiwon lafiya na duniya karo na 70 da aka yi jiya a birnin Geneva, wadannan 'yan takara uku sun yi bayani daya bayan daya, game da ra'ayoyi gami da manufofinsu kan raya hukumar WHO, daga bisani mambobin WHO 194 suka jefa kuri'a. A karshe, tsohon ministan harkokin wajen kasar Habasha, wato Dokta Tedros Adhanom ya lashe zaben inda ya zama sabon babban darekta na hukumar WHO, wanda zai maye gurbin Madam Margaret Chan wadda aka zaba kan wannan tun ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2007. Tedros Adhanom zai kama aiki daga ranar 1 ga watan Yulin bana, inda zai yi wa'adin shekaru biyar.

A wajen bikin rantsar da shi, darekta janar na WHO mai ci, Tedros Adhanom ya bayyana cewa:

"Ni, Tedros Adhanom, na yi alkawarin nuna himma da kwazo wajen gudanar da aikina da sunan WHO kuma bisa manyan muradun hukumar, ba zan amince da duk wani umurni ko roko daga wasu gwamnatoci gami da kungiyoyi ba, zan yi kokarin sauke nauyin dake kaina tare da kammala aikina yadda ya kamata."

Dokta Tedros Adhanom ya kuma gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya dauki alkawarin cewa, zai jagoranci hukumar WHO don samar da kyakkyawar hidima ga membobinta, da tinkarar kalubalolin da kasa da kasa ke fuskanta ta fuskar kiwon lafiya.

Dokta Tedros ya ce:

"Ina farin-ciki sosai saboda zan kama aiki daga ranar 1 ga watan Yuli, zan yi kokarin fito da wasu muhimman shirye-shirye don shawo kan kalubalolin da muke fuskanta. Kun san wannan ba abu ne mai sauki ba, gaskiya akwai wahala. Muna bukatar ra'ayi, da alkawari gami da goyon-bayanku, akwai bukatar mu yi aiki tare da ku, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu. Ina nuna matukar godiya ga dukkanin kasashe membobin hukumar WHO saboda cikakken goyon-bayan da suka nuna mini."

A cikin jawabin da ya gabatar, Dokta Tedros ya kuma ya jaddada cewa, hukumar WHO za ta dukufa wajen karfafa hadin-gwiwa da kowa, da kara samar da hidimomin jinya ga al'ummar kasa da kasa, musamman ma al'ummomin dake da bukatar jinya sosai. Bugu da kari, ya kamata a ci gaba da yin garambawul ga ayyukan hukumar WHO, ta yadda za'a samu nasarori yayin gudanar da aiki. Tedros ya ce, yana fatan hukumar kiwon lafiya ta WHO za ta kara kyautata lafiyar dan Adam, don haka, zai shugabanci WHO don cimma wannan babban buri.

Har ila a yayin bikin, wakilai daga wasu shiyyoyi shida da kasashe sun gabatar da jawabi daya bayan daya, inda suka taya Tedros Adhanom murnar lashe zaben babban darekta hukumar ta WHO, kuma suna fatan zai jagoranci WHO wajen tinkarar duk wani kalubale ta fannin kiwon lafiya a fadin duniya. Wakilan sun kuma nuna godiya ga kokarin da tsohuwar darekta janar ta WHO wato Madam Margaret Chan ta yi a cikin shekaru goman da suka gabata.

Dokta Tedros Adhanom ya rike mukamin ministan kiwon lafiya na kasar Habasha daga shekara ta 2005 zuwa 2012, kana daga shekara ta 2012 zuwa ta 2016, ya zama ministan harkokin wajen kasar. Bayan haka kuma, ya taba zama shugaban asusun a yaki da cutar kanjamau da tarin fuka gami da zazzabin cizon sauro na malariya, da shugaban kwamitin kulla huldar abokantaka ta fannin yaki da malariya da sauransu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China