A sanarwar da aka fitar, Mr. Guterres ya ce, gudummawar da aka bayar ba za ta kai ga biyan bukatun mutane miliyan 130 a duniya ta fannin agajin jin kai ba, don haka, ya kamata a kulla abokantaka a yunkurin magance tare da kawo karshen rikice-rikice da kyautata kwarewar tinkarar bala'u, tare da kawar da matsalar daga tushe. Mr. Guterres ya kara da cewa, ya ji dadin kokarin da aka yi wajen cika alkawuran da aka dauka a gun taron, kuma ya yi kira ga sassa daban daban da su ci gaba da wannan kokari, don kara cimma nasara a wannan bangare.(Lubabatu)